Ka Maka ni a Kotu Idan Sharri Nake Maka: Wike Ya Jaddada Cin Rashawar Ayu

Ka Maka ni a Kotu Idan Sharri Nake Maka: Wike Ya Jaddada Cin Rashawar Ayu

  • Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya kalubalanci Iyorchia Ayu kan ya kai shi kotu idan sharri yayi masa a kan zarginsa da rashawa da yake
  • Wike yace babu wani kamfen da Ayu ya isa ya jagorance shi kuma ta yaya zai iya yakar rashawa bayan dumuzgu yake a cikinta
  • Wike ya jaddada zargin shugaban jam’iyyar da yake da karbar N1 biliyan daga ‘dan takarar shugaban kasa da wata N100m daga wani Gwamna kan aikin da jam’iyyar ta riga ta biya

Ribas - Nyesom Wike, Gwamnan jihar Ribas ya kalubalanci Iyorchia Ayu, shugaban jam’iyyar PDP na kasa, kan ya kai shi kotu idan bashi da hannu a zargin rashawa da yake masa, jaridar TheCable ta rahoto.

Gwamnan jihar Ribas
Ka Maka ni a Kotu Idan Sharri Nake Maka: Wike Ya Jaddada Cin Rashawar Ayu. Hoto daga TheCable.ng
Asali: UGC

Gwamnan yayi maganar a ranar Asabar a filin wasa na Adokiye Amiesimaka yayin kaddamar da kamfen din jihar na PDP.

Kara karanta wannan

Ayu Barawo Ne, Ya Fara Gina Jami'a a Jihar Benue: Nyesom Wike

Wike da mukarrabansa suna ta bukatar murabus din Ayu saboda an yin karantsaye ga kundin tsarin jam’iyyar ganin cewa shi da ‘dan takarar shugaban kasa sun fito daga yanki daya.

Ayu ‘dan asalin jihar Binuwai ne wacce take arewa ta tsakiya yayin da Atiku Abubakar, ‘dan takarar shugabancin kasa na PDP ya fito daga Adamawa, yankin arewa maso gabas na Najeriya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A watan Oktoba, Gwamnan jihar Ribas ya zargi shugaban PDP da zama maciyin rashawa kuma baya iya bayyana yadda aka yi da kudin dake asusun jam’iyyar.

Ya zargi Ayu da karbar kudi har N1 biliyan daga ‘dan takarar shugabancin kasa da wata N100 miliyan daga wani gwamna don yin wani aiki da tuni jam’iyyar ta biya.

Channels TV ta rahoto, Sai dai shugaban jam’iyyar ya musanta dukkan wadannan zargin.

Kara karanta wannan

Wike Ya Sake Tada Kura, Ya Ce PDP Za Ta Gane 'Khaki Ba Leda Bane'

Ayu ya wawuri kudi, Gwamna Wike

Har ila yau, a yayin kaddamar da yakin neman zaben, Wike ya sake jaddada zargin inda ya kara da cewa Ayu bai dace da shugabancin tawagar kamfen din PDP.

“Babu wanda zai saurari kamfen din da maciyin rashawa ke jagoranta. Ayu maciyin rashawa ne. Jama’ar Ribas suna takaici. Ayu kana yakar rashawa, ta yaya kake yaki da rashawa? Nace ka saci N1 biliyan. Nace ka kwashe kudi daga cikin wadanda muka samu daga zaben fidda gwani. Ayu ka maka ni a kotu.”

- Wike yace.

“Baka isa kayi yaki da jihar Ribas ba kuma kayi nasara.
“Ayu ba zaka iya jagoranta ta ko jihar Ribas ba zuwa kowanne kamfen saboda kana cin rashawa.”

- Wike ya jaddada.

Ayu Barawo ne, ya fara gina jami’ a Benue, Wike

A wani labari na daban, Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya fallasa cewa Iyorchia Ayu, Shugaban PDP na kasa ya fara gina katafariyar jami’ a Binuwai.

Ya ayyana shugaban jam’iyyar adawan da zama babban barawo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng