Sufetan Yan Sanda Na Kasa Ya Sa Labule Da Jagororin Jam'iyyu 18 Kan 2023

Sufetan Yan Sanda Na Kasa Ya Sa Labule Da Jagororin Jam'iyyu 18 Kan 2023

  • Shugaban rundunar 'yan sanda na ƙasa ya shiga ganawa da jagororin jam'iyyun siyasa 18 kan abinda ya shafi 2023
  • IGP Usman Baba, yace wannan taron ya zama tilas biyo bayan matsalolin da ake samu na kai hari Ofisoshin INEC da rikicin siyasa
  • A baya-bayan nan mahara sun farmaki Ofishin hukumar zaɓe ta ƙasa a jihohin Ogun da Osun

Abuja - Sufeta Janar na rundunar yan sandan ƙasar nan, IGP Usman Alƙali Baba, ya shiga ganawar sirri yanzu haka da shugabannin jam'iyyun siyasa 18 kan tsaro da magance rikicin siyasa gabanin 2023.

Jaridar Punch tace taron wanda ke gudana a Hedkwatar yan sanda dake Abuja zai tattauna batutuwan da suka shafi hare-haren da aka kai Ofisoshin INEC kwanan nan da sauran matsalolin da suke alaƙa da siyasa.

IGP Usman Alkali Baba.
Sufetan Yan Sanda Na Kasa Ya Sa Labule Da Jagororin Jam'iyyu 18 Kan 2023 Hoto: Punchng
Asali: UGC

An tattaro cewa shugaba kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar AAC, Omoyele Sowore, shugaban PDP, Iyorchia Ayu, Sakataren tsare-tsare na APC, Suleiman Argungu, na cikin waɗanda suka wakilci jam'iyyunsu.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Tona Masu Lallaban Shi Wajen Samun Takarar Mataimakin Shugaban Kasa

Haka zalika daga cikin waɗanda suka halarci taron harda kwamishinan INEC, Barista May Agbamuche-Mbo, Darakta Janar na hukumar tattara bayanan sirri, Ahmad Rufai, da wasu wakilan hukumomin tsaro da sauransu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa IGP ya shirya taron?

Da yake hira da manema labarai jim kaɗan kafin fara taron a sirrance, IGP yace kiran zaman ya zama dole sakamakon abubuwan dake wakala wanda idan ba'a dakile su ba zasu dagula lissafin tsaro da zaɓe.

Daily Trust ta ruwaito IGP na cewa:

"Rikicin siyasa ya kasu gida uku, na farko shi ne wanda ake harin jami'ai da kayayyakin INEC kamar yadda mutane suka shaida a Osun da Ogun a 'yan kwanakin nan."

"Na biyu kuma shi ne rashin hakuri tsakanin jam'iyyu da kuma na karshe rikicin siyasa da ya saba aukuwa a wurin Kamfe, zaɓe da kuma bayan zabe."

Kara karanta wannan

An gamu: Tinubu ya gana da CAN kan muradai da buktun Kiristocin Najeriya

"Kididdiga ta nuna cewa aƙalla an samu Kes ɗin rikicin siyasa 52 a tsakanin jam'iyyu a faɗin jihohi 22 tun daga ranar da aka buɗe yakin neman zaɓen 2023, watau 28 ga watan Satumba, 2022."

A wani labarin kuma a hanyar zuwa taron siyasa, Ayarin kwamishinan kananan hukumomi da naɗin sarauta na jihar Bauchi sun samu hatsari a Titin Miya-Wurji

Rahoton hukumar kiyayye haɗurra (FRSC) ya nuna cewa mutum biyu sun rasa rayukansu yayin da wani ɗaya ke kwance a Asibiti.

Kwamishinan, Abdulrazaq Nuhu Zaki, da kansa tare da taimakon FRSC da yan sanda ne suka ɗauki mutanen zuwa wani babban Asibiti.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262