Zaɓen Shugaban Ƙasa Na 2023: Jerin Buƙatun Da Shugabannin CAN Suka Gabatarwa Tinubu A Abuja
FCT, Abuja - Gabanin zaben shugaban kasa na 2023, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, ya gana da shugabannin kungiyar kiristocin Najeriya, CAN, a Abuja.
CAN tunda farko ta nuna cewa ba ta goyon bayan tikitin musulmi na musulmi na jam'iyyar APC ta yi bayan zaben Kashim Shettima, tsohon gwamnan jihar Borno a matsayin abokin takararsa.
Amma, yayin ganawarsa da shugabannin CAN karkashin sabon shugabanta Daniel Okoh, Tinubu ya yi bayanin dalilin da yasa ya zabi Shettima kuma ya bada shugabannin kiristocin cewa ba zai yi gwamnati na nuna wariyar addini ba idan an zabe shi a 2023.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Bayan sauraron dan takarar shugaban kasar na APC, shugabannin CAN sun gabatarwa da bukatunsu gare shi, a cewar wata sanarwa da hadimin Tinubu, Tunde Rahman ya aike wa Legit.ng a ranar Laraba, 13 ga watan Nuwamba.
A cikin bukatun akwai:
1. Yan sandan jiha ko kuma rundunar yan sanda wacce ba tarayya ke kula da ita ba
2. Ba wa jihohi karfin iko
3. Daidaito da bawa dukkan addinai hakokinsu
4. Ba wa dukkan kabilu ikon cin gashin kansu
5. Ba wa garuruwa ikon kula da albarkatunsu
6. Rashin amincewa da kiwo a fili
7. Tsarin zabe wanda zai ba wa kowa damar yin zabe da kuma a zabe shi/ita
2023: Allah zai hukunta mu idan ba mu goyi bayan Tinubu ba, CAN na Legas
Tunda farko, Legit.ng ta rahoto cewa shugabannin kungiyar kirista na Najeriya, CAN, a Legas ta bayyana goyon bayanta ga Tinubu.
An rahoto cewa sun bayyana hakan ne a ranar Lahadi, 16 ga watan Oktoban 2022, ta baki shugaban CAN na Legas, Rabaran Stephen Adegbite.
Zaben 2023: Tinubu Ya Nuna Bajintarsa Ta Rawar Da Ba A Saba Gani Ba Yayin Da APC Ta Kaddamar Da Kamfen A Filato
Adegbite ya ce Allah zai musu hukunta kungiyar addinin na Legas idan ba ta goyi bayan Tinubu ba.
Asali: Legit.ng