2023: Gwamnatin PDP Zata Hada Kan 'Yan Najeriya, In ji Atiku
- Dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar ya sake ba yan Najeriya tabbacin cewa zai ciyar da kasar gaba idan aka bashi dama
- Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce gwamnatinsa zata mayar da hankali wajen hada kan kasar da wanzar da aminci a tsakanin al’ummarta
- Atiku ya ce idan har ya dare kujerar shugaba Buhari toh zai kafa gwamnati mai hada kan kasa
Lagos - Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, ya dauki alkawarin hada kan ‘yan Najeriya tare da tabbatar da yancin yan jarida idan ya lashe zaben shugaban kasa.
Atiku ya dau alkawarin ne a ranar Laraba, 16 ga watan Nuwamba, lokacin da ya zanta da kungiyar editocin Najeriya a jihar Lagas, jaridar Punch ta rahoto.
Da yake jawabi ga editocin, tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi alkawarin cewa idan har ya dare kujerar Buhari, gwamnatinsa zata kafa ‘gwamnati mai hada kan kasa’.
Ya ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“A 1999, mun kasance da yan takarar shugaban kasa biyu daga kudu kuma PDP ta yi nasara sosai amma mun samu gwamnati mai hada kan kasa.
“Mun kasance da ministoci daga jam’iyyun APP da AD sannan kasar ta zamo tsintsiya madaurinta daya kuma hakan ya samar da zaman lafiya da kwanciyar hankalin da muke muradi. Wannan shine abun da nake burin yi.
“PDP zata kafa gwamnati mai hada kan kasa. Hakan na daya daga cikin hanyoyin hada kan kasar nan. Za a tafi da kowani bangare da yanki wajen nade-naden mukamai a kowace ma’aikata.”
Da aka tambaye shi game da tanadin da ya yiwa tattalin arzikin Najeriya, Atiku ya ce yana niyan ci gaba da manufar tattalin arzikin gwamnatin PDP a 1999-2007 wadanda suka hada da daidaita tattalin arzikin, tallafawa kamfanoni masu zaman kansu.
Har ila yau, Atiku ya ce zai ci gaba da manufar siyar da hannun jari ga yan kasuwa na gwamnatin Olusegun Obsanjo, rahoton Vanguard.
A nashi bangaren, darakta janar na kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa na PDP, Gwamna Aminu Tambuwal ya yi godiya ga kafafen watsa labarai kan rawar ganin da suke takawa wajen karfafa damokradiyya a Najeriya.
Tambuwal ya kuma bukaci kafafen watsa labarai da su kasance marasa daukar bangare a siyasa yayin kawo rahoto daga dukkan bangarori gabannin babban zabe mai zuwa.
Asali: Legit.ng