2023: Sanatan PDP Ya Mance da Atiku, Ya Yaba Wa Dan Takarar Shugaban Kasa Na APC

2023: Sanatan PDP Ya Mance da Atiku, Ya Yaba Wa Dan Takarar Shugaban Kasa Na APC

  • Sanata mai wakiltar mazaɓar Enugu ta gabas a majalisar dattawa, Chimaroke Nnamani, ya sake yabon Tinubu na APC
  • Tsohon gwamnan yace lokacin da Tinubu ke matsayin gwamnan Legas ya taka muhimmiyar rawa wurin inganta tsarin Shari'a
  • APC ta sanya sunan Sanata Nnamani a cikin kwamitin kamfen Tinubu amma sunayen karshe da ta fitar ta cire sunansa

Enugu - Sanatan jam'iyyar PDP daga jihar Enugu, Chimaroke Nnamani, ya cigaba da sakin jerin kalaman yabo ga ɗan takarar shugaban kasa a inuwar APC, Bola Ahmed Tinubu.

Jaridar Premium Times tace a wannan karon, Sana Nnamani, ya yaba wa Tinubu ne kan ɗumbin nasarorin da ya samu a ɓangaren shari'a lokacin yana matsayin gwamnan Legas daga 1999-2007.

Tinubu da Sanata Nnamani.
2023: Sanatan PDP Ya Mance da Atiku, Ya Yaba Wa Dan Takarar Shugaban Kasa Na APC Hoto: Bola Tinubu, Chimaroke Nnamani
Asali: Facebook

A cewarsa, gwamnatin Legas karkashin Tinubu ta aiwatar da mafi yawan shawarin da kwamitin shari'a ya gabatar, ciki har da kawar da cin hanci a ɓangaren shari'a.

Kara karanta wannan

2023: Kada Yan Najeriya Su Cire Rai, APC Zata Kawo Canjin da Suke Bukata, Tinubu

Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da Sanata Nnamani ya rattaɓawa hannu kuma aka raba wa manema labarai.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa wannan ba shi ne karon farko da Mista Nnamani, tsohon gwamnan Enugu, ya fito fili ya nuna goyon baya da "Tallata" Tinubu ba duk da kasancewar mamban PDP.

Wannan sanarwa ta fito ne kwanaki uku bayan Sanatan ya bukaci Igbo su daina faɗa da Yarbawa, su fara duba yuwuwar ganin Tinubu ya kafa gwamnati a Najeriya.

Tun da farko dai sunansa na cikin waɗanda jam'iyyar APC ta fitar a kwamitin yakin neman zaɓen shugaban kasa daga bisani aka cire sunan bayan dogon nazari.

Wasu daga cikin nasarorin Tinubu

Sanatan, mai wakiƙtar mazaɓar Enugu ta gabas, yace bayan inganta walwala da jin dadin Alƙalai, Tinubu ya yi kokarin wajen tsaftace hanyar ɗaukar sabbin ma'aikata a ɓangaren shari'a.

Kara karanta wannan

Rabin Albashi: Badaru Ya Bayyana Kokarin da Suke Tsakanin ASUU da FG

Yace na daga cikin nauyin da ya ɗora ƙungiyar Lauyoyin (NBA) reshen jihar Legas ta tabbatar an gudanar da naɗe-naɗen sashin shari'a da ɗaukar aiki ta hanyar cancanta da kuma shawarin hukumar Shari'a.

Kazalika NBA ta yi kokarin gudanar da bincike kan duk wasu ƙorafe-ƙorafe da aka shigar kan Alkalai da dukkanin matakan shari'a.

Sanatan bai tsaya nan ba, ya ƙara da cewa Tinubu ya taimaki ƙungiyoyi masu zaman kansu wajen shirya tarukan ƙara wa juna sani kan haƙƙin ɗan Adam da shugabanci nagari da nufin wayar da kan mutane su san nauyin dake kansu.

Yace:

"Game da inganta ayyukan majalisa da dokoki, majalisar Legas ta tsaya tsayin daka wurin ganin kowa na ganin abinda ke tafiya ba ɓoye-ɓoye."
"Haka nan majalisar ta kafa dokar kirkirar shafin yanar gizo ga ma'aikatar sharia a matsayin wani yunkuri na jawo hankalin al'umma kan dokoki."

Obidient babbar barazana ce ga PDP a 2023 - Soludo

Kara karanta wannan

Karshen rikicin PDP: Wani tsohon shugaban kasa zai sulhunta Atiku da tawagar Wike

A wani labarin kuma Peter Obi Ya Samu koma baya biyo bayan matakin gwamnan Anambra na goya wa jam'iyyarsa baya a zaɓen 2023

Gwamna Soludo, ya tabbatar da cewa zai yi wa ɗan takarar shugaban kasa a inuwar APGA, Peter Umeadi, aiki a zaɓe mai zuwa.

A cewarsa takarar Peter Obi a LP da tafiyar magoya bayansa da ake kira Obidients ba abinda zasu iya wa APGA sai dai sun kasance barazana ga jam'iyyar PDP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262