Tinubu: Kada ‘Yan Najeriya Su Yanke Kauna Da APC, Za Mu Yi Abun da Ya Fi Na Baya

Tinubu: Kada ‘Yan Najeriya Su Yanke Kauna Da APC, Za Mu Yi Abun da Ya Fi Na Baya

  • Gabannin babban zaben 2023, dan takarar shugaban kasa na APC, Asiwaju Bola Tinubu ya roki yan Najeriya a kan kada su yanke kauna da jam'iyyarsa
  • Tinubu ya bayar da tabbacin cewa za su kara azama wajen kawo canjin da yan Najeriya ke bukata a nan gaba
  • Tsohon gwamnan na jihar Lagas ya kuma jinjinawa mahaifinyar Gwamnna Rotimi Akeredolu kan tsayin dakan da tayi wajen tarbiyantar da 'ya'yanta lokacin da take raye

Ondo - Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ya bukaci yan Najeriya da kada su yanke kauna da jam’iyyar mai mulki a kasar.

Da yake jawabi a ranar Asabar a wajen bikin binne Grace Akeredolu, mahaifiyar Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo a Owo, Tinubu ya ce APC zata kara himma don inganta rayuwar ‘yan Najeriya, jaridar TheCable ta rahoto.

Kara karanta wannan

2023: Ka yanke kawai kaine shugaban 'yan Najeriya na gaba, shugaban APC ga Tinubu

Bola Tinubu
Tinubu: Kada ‘Yan Najeriya Su Yanke Kauna Da APC, Za Mu Yi Abun da Ya Fi Na Baya Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Tsohon gwamnan ya ce:

“Alhamdulillahi gamu a raye. Ana iya samun tangarda ko akasi a wajen jiran tsammani. Babu wanda ke son ace ya gaza.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Ba za ku iya yanke kauna da mu ba. Za mu kara himma. Za mu bayar da gudunmawa don ganin ci gaban da kuke so.”

Dan takarar shugaban kasar ya ce mahaifiyar Akeredolu ta bar tarihi mai kyau.

A nashi bangaren, shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda ya samu wakilcin mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ya ce rayuwar mahaifiyar Akeredolu ta cancanci ayi mata murna.

Ya ce:

“Yau ranar farin ciki ce. Mun kai gabar da dole mu yi bukin murna na daya daga cikin masu daraja. Lokaci ne na taya Mama murna saboda ayyukan aklhairi da tayi.
“Rayuwar Garce Akeredolu rayuwa ce da ta cancanci ayi murna da ita. Ta rasa mijinta tana da shekaru 50 sannan ta ci gaba da rayuwar har ta kai shekaru 90. Ta tarbiyantar da yaranta. Ta yi namijin kokari wajen rainon yara maza hudu.

Kara karanta wannan

Gwamnonin PDP Da Suka Bayar Da Sharudda A Bainar Jama'a Kafin Yi Wa Atiku Aiki A Jihohinsu

“Shakka babu ta yi kokari sosai. Dole mu godewa Allah saboda ba kawai rainon yaran tayi ba, dukkansu sun daukaka a rayuwa.”

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa tsohon gwamnan jihar Ekiti, Dr Kayode Fayemi da matarsa, Erelu Bisi, Sanata Ibikunle Amosun, Dr Olusegun Mimiko sun sun hallara a wajen taron.

Sauran manyan da suka halarci taron harda ministan kimiyya da fasaha Dr. Olorunnimbe Mamora da ministan matasa da wasanni, Sunday Dare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng