Babban Malamin Addini Ya Yi Sabon Hasashe Game Da Zaben 2023, Ya Aike Sako Ga Shugaban INEC
- An bukaci shugaban hukumar zabe na kasa, Mahmood Yakubu, da ya wajabtar yin amfani da na’urar BVAS a zaben 2023
- Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Elijah Ayodele ne yayi wannan kira
- Ayodele ya bukaci INEC da kada ta bari jam’iyyun siyasa su hana ta amfani da na’urar BVAS a babban zabe mai zuwa
Shugaban coxin INRI Evangelical Spritual, Primate Elijah Ayodele, ya yi gagarumim gargadi ga shugaban hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta, Mahmood Yakubu, game da babban zaben 2023 mai zuwa.
A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun hadimin labaransa, Osho Oluwatosin, Primate Ayodele ya gargadin shugaban na INEC da kada ya bari jam'iyyun siyasa su tsoma baki a cikin harkokin hukumar, jaridar PM News ta rahoto.
Babban faston ya magantu kan batun tura sakamakon zabe ta na'ura, yana mai cewa kada INEC ta bari a cire tsarin a zaben.
Karin Bayani: Gwamnatin Najeriya Ta Sake Maka Nnamdi Kanu A Kotu, Ta Gabatar Da 'Sabbin' Tuhume-Tuhume 7
Ka zamo mai kishi don dorewar hadin kan Najeriya - Primate Ayodele ga shugaban INEC
Primate Ayodele ya bayyana cewa zaben 2023 zai yanke hukunci kan ko Najeriya zata ci gaba da kasancewa tare kuma cewa shugaban INEC na da gagarumar rawar gani da zai taka wajen yanke wannan hukinci.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya shawarce shi da ya ci gaba da kasancewa mai kishi don hadin kan Najeriya, rahoton Daily Post.
Ya ce:
"Kada INEC ta kuskura ta bari a cire na'urar BVAS a zaben 2023, ya zama dole shugaban hukumar ya tsaya tsayin daka saboda wannan zai bashi. Zaben na da muhimmanci, zai bamu damar sanin ko Najeriya zata ci gaba da zama tsintsiya madaurinki daya, don haka ya zama dole shugaban na INEC ya zama mai kishi. Yana da gagarumar rawar ganin da zai taka."
Malamin addinin ya kuma ce wasu yan takara na shirin haddasa rikici a kasar nan idan basu ci zabe ba.
Ya bayar da shawarar cewa a gargadi jam'iyyun siyasa saboda babu wanda ke da ikon nasara a zabe.
Talaka zai sha jar miya idan na karbi mulki a hannun Buhari, Atiku ga matasa
A wani labarin, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya dauki alkawarin cewa idan har ya zama shugaban kasa zai budewa matasa hanyoyin samu koda kuwa a gidansu talauci ya kare
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya kuma hango shafewar jam'iyyar APC bayan 2023 domin a cewarsa PDP kadai ce jam'iyyar da ya sani a Najeriya.
Asali: Legit.ng