Rikicin APC: Gwamna Ganduje Ya Shiga Tsakanin Garo da Doguwa

Rikicin APC: Gwamna Ganduje Ya Shiga Tsakanin Garo da Doguwa

  • A kwanakin baya ne dai aka samu rashin jituwa a tsakanin Hon. Murtala Sule Garo da kuma Alhassan Ado Doguwa
  • Sai dai a ranar Litinin ɗin da ta gabata ne, gwamnan jihar Kano ya shiga tsakaninsu tare da yi musu sulhu
  • Tuni dai Doguwa ya tabbatar da cewa ya yafe wa duk wanda suka samu saɓani da shi tare da tabbatar da haɗa kai da kowa da kowa a zaɓe mai zuwa na 2023

Kano - Jaridar DailyTrust ta rawaito cewa, Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya shiga tsakanin ɗan takarar mataimakin gwamna na jihar Kano, Murtala Sule Garo da shugaban masu rinjaye na Majalisar Wakilai, Hon. Alhassan Ado Doguwa.

A kwanakin baya ne dai aka zargi Doguwa da cin zarafin Hon. Murtala Sule Garo tare da raunata shi a yayin gudanar da wani taro na masu ruwa da tsaki na jam'iyyar ta APC.

Kara karanta wannan

2023: 'Komai Ya Zo Karshe' Bukola Saraki Ya Magantu Kan Sasanta Atiku da Wike a PDP

Kodayake, Doguwa ya musanta wannan batu. Sai dai ya sha alwashin cigaba da fafatawa da Garo ɗin a jam'iyyance.

Sai dai shugaban jam'iyyar APC na jahar Kano,Alhaji Abdullahi Abbas, a ranar Talata, ya tabbatar da cewa Gwamna Ganduje ya yi nasarar sulhunta tsakanin ɓangarorin biyu.

Jam’iyyar
Rikicin APC: Gwamna Ganduje Ya Shiga Tsakanin Garo da Doguwa
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewar Abdullahi Abbas;

"Ina mai tabbatar muku ba mu da wani sauran rikici a wannan jam'iyyar tamu. An riga an sulhunta tsakanin Alhassan Duguwa da Murtala Sule Garo. Komai ya wuce kuma yanzu, muna nan a matsayin tsintsiya maɗaurinki ɗaya."

Sannan Shugaban Jam'iyyar ya tabbatar da cewa za su cigaba da yin aiki tare domin tabbbatar da nasarar jam'iyyar a zaɓe mai zuwa na 2023.

Da yake bayyana ra'ayinsa kan wannan al'amari, Doguwa ya tabbbatar da faruwar wannan sulhu tare da tabbatar da cewa, komai ya wuce.

Kara karanta wannan

Karshen rikicin PDP: Wani tsohon shugaban kasa zai sulhunta Atiku da tawagar Wike

Sannan za su yi aiki tare da kowa da kowa domin tabbatar da nasarar jam'iyyar.

"Mai girma gwamna,Abdullahi Ganduje ya riga ya sulhunta mu da Garo, sannan Nasiru Aliko Koki da kuma shugaban jam'iyyar sun samu halartar wannan zama da aka yi a ranar Litinin da misalin ƙarfe huɗu na yamma,"

….. in ji Doguwa.

Haka kuma ya bayyana cewa;

"mun yi nazarin wannan rashin fahimta tare da ba wa juna haƙuri. Gwamna kuma ya yi mana kalamai masu daɗi tare da nuna mana inda duk muka yi kuskure. Sannan ya tabbatar mana cewa duk 'ya'yansa ne."

A cewar doguwa, ya yafewa kowa da kowa da sauran mambobin da magoya bayan da suka ɓata masa rai, inda ya kuma nemi su ma su yafe masa.

A wani labarin kuma: Shugaban masu rinjaye na majalisar wakilan tarayya, Alhassan Ado Doguwa, yace wasu mutane da ya ayyana da 'yan daban siyasa sun farmaki tawagarsa a kofar Filin Jirgin Malam Aminu Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida