Rikici Na Kara Tarwatsa PDP, Atiku Ya Yi Rashin Babbar Jigo a Jihar Gombe
- Wata tsohuwar shugaba a jam'iyyar PDP reshen shiyyar arewa maso gabas, Mole Istifanus, ta fice daga jam'iyyar
- A wata wasika da ta aike wa shugaban PDP na gundumarta a jihar Gombe, ta gode wa kowa da kowa PDP bisa damar da aka bata ta bayar da gudummuwa
- Duk da bata bayyana ainihin dalilin ɗaukar wannan matakin ba, ana ganin hakan na da alaƙa da rikicin da ya addabi PDP a Gombe
Gombe - Yayin da rikicin cikin gida ke cigaba da tarwatsa jam'iyyar PDP, wata jigo kuma tsohuwar shugaba a PDP shiyyar arewa maso gabas, Misis Mole Istifanus Bennet, ta yi murabus daga jam'iyyar a Gombe.
Jaridar Trbune tace Mole Istifanus, wacce bata jima da sauka kujerar shugabar matan PDP a Gombe ba, ta yi gum bata faɗi dalilin daukar wannan mataki ba.
Amma ana tsammanin ficewarta daga PDP ba zai rasa alaƙa da yadda jam'iyyar ke tafiyar da harkokinta a jihar ba musamman a yan kwanakin nan.
Wasiƙar murabus ɗin na ɗauke da kwanan watan 3 ga watan Nuwamba, 2022 da kuma Adireshin shugaban PDP na mazaɓarta gundumar Kaltungo ta yamma kuma tuni sakon ya isa ga PDP.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ta kuma gode wa jam'iyyar bisa damar da aka bata har ta bayar da gudummuwa iyakar karfinta har zuwa yau 3 ga watan Nuwamba, 2022, lokacin ta fita daga PDP.
Wani sashin wasikar tace:
"Ina mai rubuta wannan wasika cikin girmamawa tare da sanar maka cewa na yi murabus daga jam'iyyar PDP daga yau. Ina mai amfani da wannan hanya wurin miƙa godiyata ga shugabannin jam'iyya bisa bani damar aiki."
Wasu bayanai sun nuna cewa ta yanke fita PDP ne sakamakon zanga-zangar da ta jagoranci mata suka gudanar kan abinda suka kira rashin adalcin da jam'iyya ke musu.
An naɗa sabon shugaban PDP a jihar Katsina
A wani labarin kuma Ana Tsaka Rikici, Jam'iyyar PDP Ta Kasa Ta Nada Sabon Shugaba a Katsina
Jam'iyyar PDP ta amince da naɗin Alhaji Salisu Lawal-Uli a matsayin shugaban reshenta na jihar Katsina.
Wannan na zuwa ne yayin da sabon rikici ya ɓalle tsakanin ɗan takarar gwamna, Yakubu Lado da tsohon shugaba, Alhaji Majigiri.
Asali: Legit.ng