2023: Lokaci Ya Yi da 'Yan Arewa Zasu Biya Tinubu Alherin da Ya Musu, Shettima
- Tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, yace lokaci ya yi da yan arewa zasu saka wa Bola Ahmed Tinubu
- Sanata Shettima, ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a APC, yace Tinubu ne ya taimaka Buhari ya lashe zaɓe sau biyu
- Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya roki al'ummar Hausawa kar su bari a yaudare su a zaɓe mai zuwa
Lagos -Ɗan takarar mataimakin shugaban kasa a inuwar APC, Sanata Kashim Shettima, yace zaɓen 2023 wata dama ce ga 'yan arewa su saka wa Bola Tinubu bisa goyon bayan da ya nuna wa yankinsu a baya.
Jaridar Premium Times ta rahoto cewa Shettima ya yi wannan furucin ne yayin da ya ziyarci al'ummar Hausawa a Alaba-Rago, ƙaramar hukumar cigaba ta Iba, jihar Legas.
Shettima ya samu rakiyar gwamnan jihar, Babajide Sanwo-Olu, da takwaransa na jihar Kano, Dakata Abdullahi Ganduje, shugaban APC na Legas, Cornelius Ojelabi, da dukkan shugabannin 'yan arewa mazauna jihar.
Yace Tinubu ne ya yi fafutukar ɗora shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari a kujerar da yake kai a zaɓen 2015 ta hanyar bashi tulin kuri'u daga kudu maso yamma, ya sake maimaita haka a 2019.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Sanata Shettima ya ƙara da cewa Tinubu ne ya taimaka wa Atiku Abubakar ya nemi zama shugaban ƙasa a zaɓe lokacin da PDP ta kori tsohon mataimakin shugaban, haka ya sake yi wa Nuhu Ribado.
A kalamansa ya ce:
"Mu mutane ne masu karamci, ya kamata mu girmama alwashin da muka ci da alƙawarin da muka ɗauka. Wannan lokaci ne da 'yan arewa zasu biya ta hanyar goyon bayan Tinubu.
Kar ku bari a yaudare ku - Sanwo-Olu
Da yake nasa jawabin, Gwamna Sanwo-Olu ya roki Hausawan kar su kuskura su bari a yaudare su kuma su tabbata sun dangwalawa APC a kuri'ar masu neman zama shugaban kasa.
Yace sun shirya wannan taron ne a wani ɓangaren tattaunawar neman goyon baya daga baƙi mazauna jihar Legas.
Ya kuma miƙa godiyarsa ga al'ummar Hausawa bisa goyon bayan da suke baiwa gwamnatinsa yayin da yake kokarin inganta rayuwar dukkanin mazauna jihar.
A wani labarin kuma Ana Tsaka Rikicin Tsagewa Biyu, Uwar Jam'iyya Ta Kasa Ta Nada Sabon Shugaban PDP a Katsina
Jam'iyyar PDP ta amince da naɗin Alhaji Salisu Lawal-Uli a matsayin shugaban reshenta na jihar Katsina.
Wannan na zuwa ne yayin da sabon rikici ya ɓalle tsakanin ɗan takarar gwamna, Yakubu Lado da tsohon shugaba, Alhaji Majigiri.
Asali: Legit.ng