PDP Ta Dakatar da Harkokin Siyasa Saboda Mutuwar Dan Davido

PDP Ta Dakatar da Harkokin Siyasa Saboda Mutuwar Dan Davido

  • Jam'iyyar PDP a jihar Osun ta sanar da dakatar da harkokin siyasa saboda rasuwar dan mawaki Davido
  • An tashi da labari mara dadi na yadda dan shahararren mawaki Davido ya tsunduma ruwa ya mutu a jihar Legas
  • 'Yan Najeriya da sauran jama'a na ci gaba da mika sakon ta'aziyya da jimami ga ahalin Davido da sauran makusantansa

Jihar Osun - Biyo bayan mutuwar Ifeanyi, dan shahararren mawakin nan Davido, jam'iyyar PDP a jihar Osun ta bayyana dakatar da dukkan wasu harkokinta na siyasa na tsawon mako guda.

Davido, wanda dan dan uwa ne ga zababben gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke ya rasa dansa ne sanadiyyar nustewa da ya yi a ramin wanka a jihar Legas, The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Mutuwar Ifeanyi: Kwankwaso, Hadimin Buhari Da Sanata Orji Kalu Sun Mika Ta’aziyyarsu Ga Davido Da Chioma

A cewar sanarwar da shugaban kwamitin rikon PDP a jihar, Dr Adekunle Akindele, jam'iyyar ta bayyana jimami da bacin rai bisa wannan mummunan lamari da ya faru da Davido.

Mutuwar dan Davido ta sa PDP dakatar da harkokinta na siyasa
PDP Ta Dakatar da Harkokin Siyasa Saboda Mutuwar Dan Davido | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Hakazalika, ta mika ta'aziyya da ban hakuri game da sakon sannu ga dangi da sauran wadanda suka kadu da samun labarin mutuwar yaron, inji TheCable.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sanarwar ta ce:

"Biyo bayan rasuwar Ifeanyi, jam'iyyar ta dakatar da dukkan harkokinta na siyasa don taya ahalin Adeleke jimamin abin da ya faru.
"Muna jimamin rasuwar danmu Ifeanyi cikin bacin baki. Muna addu'ar Allah ya hutar da ruhinsa. Rana ce ta bakin ciki amma mun mika komai ga ubangijin duniya.
"Muna mika ta'aziyya ga Davido, matashin jakadanmu. Muna kuma taya babanmu jigo, Dr Deji Adeleke da sauran ilahirin ahalin Adeleke. Muna addu'ar Allah ya ba ahalin hakurin wannan babban rashi da suka yi."

Kara karanta wannan

Ministan farko na sufurin jiragen sama a Najeriya, babban mai kare Nnamdi Kanu ya rasu

Mbazulike Amechi, Ministan Sufurin Jiragen Sama Na Farko a Najeriya, Ya Rasu

A wani labarin, ministan farko na ma'aikatar sufurin jiragen sama a Najeriya, Cif Mbazulike Amechi ya riga mu gidan gaskiya, rahoton The Nation.

A cewar wata majiyar dangi daga bakin Ezeana Tagbo Amechi na karamar hukumar Nnewi ta Kudu a jihar Anambra, tsohon dan siyasar ya rasu ne a yau Talata 1 ga watan Nuwamba da sanyin safiya.

Rahotannin da muke samu sun bayyana cewa, jigon na Kudu shine mutum na karshe da ya saura a tafiyar Zikist, kuma ya zama minista ne a lokacin yana da shekaru 29, ya rasu yana da shekaru 93.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.