2023: Atiku Ya Kara Shiga Matsala, Jigo Ya Ayyana Cewa PDP Ta Rasa Kashi 85 Na Masoyanta
- Mista Katch Ononuju yace kusan kashi 85 cikin ɗari da mutanen da suka saba goyon bayan PDP sun koma inuwar LP
- Jigom jam'iyyar LP da Peter Obi ke neman takarar shugaban kasa, yace ya fice PDP ne saboda tarin matsaloli
- A cewarsa, Jam'iyyar LP ba kamar PDP da APC bace, zata haɗa kan yan ƙasa kuma ta jawo kowa a jiki
Lagos - Jigon jam'iyyar Labour Party (LP), Katch Ononuju, ya yi ikirarin cewa jam'iyyarsa ta gaje sama da kashi 85 na mutanen da suka saba kaɗa wa jam'iyyar PDP kuri'unsu duk zaɓe.
Yace jam'iyyar Labour Party zata yi amfani da wannan damar da ta samu wajen tabbatar da nasarar ɗan takarar shugaban kasa, Peter Obi, a zaɓe mai zuwa a watan Fabrairu, 2023.
Mista Ononuju ya bayyana haka a cikin shirin Sunrise Daily na kafar watsa labarai Channels TV ranar Litinin, 31 ga watan Oktoba, 2022.
Jigon yace:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Kusan kaso 85 cikin 100 na mutanen da a tarihi suke zaɓen PDP a yanzu sun koma inuwar LP, karku damu da abinda wasu ke faɗa da kuma kokarin ɗaukar hayar mutane, zamu yi aiki ne da na zahiri, mutanen Najeriya."
Meyasa shi kansa Ononuju ya fice PDP?
Mista Ononuju, wanda a baya-bayan nan aka naɗa shi mashawarci na musamman kan harkokin yaɗa labarai ga Obi, yace ya bar PDP zuwa LP ne saboda yadda jam'iyyar ke karbuwa a wurin mutane musamman matasa.
"Ba'a san jam'iyyar LP ba a watanni shida da suka gabata idan aka yi la'akari da yanzu, matsaloli suka ja Obi ya bar PDP, ba wai shi kaɗai bane da yawan mutane sun koma LP."
"Ba zato matasa suka kalli mutanen da suka koma cikin jam'iyyar kana suka ce nan ne ya dace mu tsunduma kuma zamu yi farin ciki da haka."
"Jam'iyyar PDP da muka gudo daga cikinta ba ta da maraba da APC a yanzu. Ita kuma LP da matasa ke fata ta zo ne da kudirin tafiya da kowa, ba wanda zafa bari a baya."
A wani labarin kuma ɗan takarar shugaban kasa a inuwar jam'iyyar AAC, Omoyele Sawore,.ya kaddamar da fara kamfe a Kano
Ɗan takarar kujera lamba daya a Najeriya karƙashin jam'iyyar AAC ya kaddamar da kamfensa a birnin Kano .
Omoyele Sawore yace komai ya lalace a mulkin APC don haka lokaci ya yi da mutane zasu gano me yake musu ciwo.
Asali: Legit.ng