2023: Babu Ɗan Tafiyar Obidients Ko Daya a Jihata, Gwamnan Ondo
- Gwamnan jihar Ondo ya yi ikirarin cewa ɗan takarar jam'iyyar LP, Peter Obi, ba shi da masu goyon bayan ko mutum ɗaya a jihar
- Da yake jawabi ta bakin mataimakinsa a Akure, Oluwarotimi Akeredolu, ya nuna cewa lokaci ya yi da mulki zai koma kudancin Najeriya
- Wasu shugabannin kungiyar Afenifere sun ayyana goyon bayansu ga takarar Bola Tinubu a zaɓe na gaba
Ondo - Gwamnan jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu, yace babu masu goyon bayan ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar Labour Party, Peter Obi, waɗanda suka fi shahara da 'Obidients' ko ɗaya a jiharsa.
Akeredolu, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Lucky Aiyedatiwa, ya yi wannan ikirarin ne a Akure yayin da ɗan takarar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya ziyarci shugabannin yarbawa.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Tinubu ya ziyarci shugabannin ƙungiyar kare al'adun Yarbawa watau Afenifere domin ya gabatar tare da yi musu bayanin manufofinsa.
Gwamnan Ondo, jihar dake kudu maso yammacin Najeriya, ya ƙara da cewa jihar ta shirya tsaf don tabbatar da mulkin Najeriya ya koma hannun ɗan kudu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Afenifere Ta Ayyana goyon baya ga Tinubu
Wasu shugabannin ƙungiyar Afenifere sun ayyana goyon bayansu ga takarar Bola Tinubu a babban zaben 2023. Lamarin da ya zo da ruɗani sakamakon Adebanjo na tare da Peter Obi.
Haka nan kuma jagororin yarbawan sun gargaɗi Tinubu kan ya yi takatsantsan, kar ya sa su yi dana sanin goyon bayan burinsa na zama shugaban ƙasa.
Da yake jawabi yayin ziyarar Tinubu, Fasoranti, yace tun farko tsohon gwamnan Legas ɗin ya nemi sanya albarkarsa a watan Afrilu amma ya faɗa masa ya je ya karɓo tikitin takara daga bisani zai sa masa Albarka.
Jaridar Vanguard ta rahoto Jagoran yarbawan yace, "Na ji daɗi yau ga shi ka dawo bayan lashe tikitin takarar shugaban ƙasa na jam'iyyarku."
Daga nan sai Fasoranti ya yi Addu'ar fatan nasara ga ɗan takarar APC a zaɓe mai zuwa kuma yana fatan zai kasance a raye domin shaida rantsar da shi a watan Mayu, 2023.
A wani labarin kuma Gwamna Makinde Ya bi sahun su Wike da Ortom, yace zasu raba gari da Atiku kan sharaɗi ɗaya
Gwamna Seyi Makinde yace matukar shugaban PDP bai yi murabus ba, to ba zai marawa Atiku baya a 2023 ba.
Gwamnan, wanda ke goyon bayan fafutukar tsagin Wike, yace ba gudu ba ja da baya game da bukatarsu ga PDP.
Asali: Legit.ng