Shugabannin Yarbawa Sun Bayyana Goyon Bayansu Ga Bola Tinubu
- Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu ya samu goyon bayan shugabannin Yarbawa
- Bola Ahmad Tinubu na ci gaba da kutsa kai a yankin Kudu maso Yamma domin neman goyon bayan shugabannin Yarbawa
- 'Yan Najeriya mazauna kasashen waje sun bayyana goyon bayansu ga dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP
Jihar Ondo - Dan takarar shugaban kas ana jam'iyyar APC, Asiwaju Bola AhmadTinubu ya samu babban abin da yake bukata domin tunkarar babban zaben 2023, Daily Trust ta ruwaito.
Duk da rasa samun goyon bayan wasu manyan kungiyoyi daga yankin Kudu maso Yamma, yanzu ya samu albarkar manyan shugabannin Yarbawa a yankin a ranar Lahadi 30 ga watan Oktoba.
Wata kungiyar hadin kan Yarbawa ta Conference of Yoruba Nationals ta bayyana goyon bayanta ga dan takarar shugaban kasa na APC.
Wadanda suka goyi bayan Tinubu
A wata ganawar da Tinubu ya yi da shugabannin Yarbawan a jihar Ondo, Tinubu ya nemi tabarruki daga shugabannin Yarbawan yankin Kudu maso Yammacin Najeriya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Daga cikin wadanda ya gana dasu sun hada da; shugaban kungiyar Afenifere, Pa Reuben Fasoranti da tsohon shugaban hafsun tsari, Janar Alana Akinrinade, rahoton Vanguard.
Hakazalika da Cif Bisi Akande, Cif Cornelius Adebayo, tsohon gwamnan Kwara, tsohon minista Cif Rufus Arogbofa da Cif Iyiola Omisore, duk sun nuna goyon bayansu ga Tinubu.
Kafin yanzu, Pa Ayo Adebanjo da farfesa Banji Akintoye sun bayyana adawarsu ga tafiyar Bola Ahmad Tinubu.
Kungiyoyi daban-daban a Najeriya sun bayyana goyon baya ga Tinubu, sai dai, wasu bangaren kiristocin Arewa suna ci gaba da nuna adawa da yadda Tinubu ya zabi abokin takara.
'Yan Najeriya Mazauna Waje Sun Bayyana Goyon Bayansu Ga Atiku, Sun Ce Ya Cancanta
A wani labarin na daban kuma, farfesa Isa Odili ya bayyana goyon bayansa ga dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2023 mai zuwa.
Ya kuma bayyana cewa, da yawan 'yan Najeriya mazauna kasashen waje sun nuna shawa'a da goyon bayansu ga Atiku Abubakar.
Odili, wanda shine daraktan kungiyar kamfen ta Atiku-Okowa Presidential Campaign Organisation ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya aikewa Legit.ng a ranar 30 ga watan Oktoba.
Asali: Legit.ng