Shugaban PDP Na Kasa Ya Maida Martani, Yace Ba Zai Zauna da Ortom Ba

Shugaban PDP Na Kasa Ya Maida Martani, Yace Ba Zai Zauna da Ortom Ba

  • Shugaban PDP na kasa, Iyorchia Ayu, ya ce ba zai nemi gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwai domin zaman sasanci ba
  • Da yake jawabi ga dattawan mahaifarsa Jemgbah ranar Asabar, Ayu ya ce ko kaɗan babu wata matsala a tsakaninsa da Ortom
  • A kwanakin baya, Gwamna Ortom ya gana da Sarakunan gargajiya na yankin da Ayu ya fito, inda ya faɗa musu sabanin da ke tsakaninsu

Abuja - Yayin da rikicin cikin gida a jam'iyyar PDP ya buɗe sabon babi, shugaban jam'iyya na ƙasa, Dakta Iyorchia Ayu, ya sha alwashin ba zai yi wani yunkurin ganawa da gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwai ba.

Ayu ya yi fatali da shawarin dattawan PDP na Jemgbah, waɗanda suka nemi shugaban jam'iyyar ya zauna da Ortom domin samun maslaha.

Kara karanta wannan

2023: Al'amura Sun Canja Yayin Da Tsohon Ministan Buhari Ya Bayyana Goyon Bayansa Ga Tinubu, Ya Bada Dalili

Shugaban PDP na ƙasa, Iyorchia Ayu.
Shugaban PDP Na Kasa Ya Maida Martani, Yace Ba Zai Zauna da Ortom Ba Hoto: vanguard
Asali: UGC

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Dakta Ayu ya hito ne daga shiyyar Jemgbah a jihar Benuwai dake arewa ta tsakiya a Najeriya.

Da yake jawabi ga dattawan mahaifarsa a Gboko ranar Asabar, Ayu ya yi watsi da shawarinsu na ya gana da gwamna Orton, inda ya nuna cewa ba shi da wata matsala da gwamnan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A kalamansa yace, "Ban da wata matsala da gwamna saboda haka ba zan nemi zama da shi ba. Ba zan je gaban wani Basarake ba da nufin neman sasanci."

Shugaban PDPn na ƙasa ya bukaci dattawan karsu yanke hukunci kan ɗan takarar shugaban ƙaa, Atiku Abubakar saboda mummunan ɗabi'ar wasu tsirarun mutane.

Daga nan kuma Ayu ya yi kira ga magoya bayan jam'iyyar PDP su zaɓi 'yan takarar PDP tun daga sama har ƙasa ciki harda Ortom dake neman zama Sanata a 2023.

Kara karanta wannan

Babban Abinda Ya Jefa Shugaban PDP Na Kasa Cikin Tirka-Tirkar Siyasa, Gwamnan Arewa Ya Magantu

Legit.ng Hausa ta rahoto muku cewa a wasu 'yan kwanaki da suka shuɗe, gwamna Ortom ya gana da dattawan mahaifar Ayu inda ya kora musu bayani kan saɓanin dake a tsakaninsa da ɗansu.

Sawore ya kaddamar da Kamfe a Kano

A wani labarin kuma ɗan takarar shugaban kasa a inuwar jam'iyyar AAC, Omoyele Sawore,.ya kaddamar da fara kamfe a Kano

Ɗan takarar kujera lamba daya a Najeriya karƙashin jam'iyyar AAC ya kaddamar da kamfensa a birnin Kano.

Omoyele Sawore yace komai ya lalace a mulkin APC don haka lokaci ya yi da mutane zasu gano me yake musu ciwo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262