Dalilin Da Yasa Shugaban PDP Na Ƙasa Ya Shiga Hatsari, Gwamna Ortom

Dalilin Da Yasa Shugaban PDP Na Ƙasa Ya Shiga Hatsari, Gwamna Ortom

  • Gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom, yace duk matsalar da shugaban PDP na ƙasa ya shiga shi ya jawo wa kansa
  • Gwamnan, yayin ganawa da wasu Sarakunan gargajiya, yace rashin cika alƙawarin Ayu ne ya haddasa rikicin PDP
  • Da yake tsokaci game da Atiku, Ortom yace ya zama dole ɗan takarar shugaban ya fito ya ba shi hakuri

Benue - Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwai ya yi ƙarin haske kan abinda ya jefa shugaban PDP na kasa, Dakta Iyorchia Ayu, cikin damuwar siyasa.

Ortom ya faɗa wa Sarakunan gargajiya na Jemgbah cewa ɗansu, Ayu, ya tsinci kansa cikin danbarwar siyasa ne saboda ƙin cika alƙawarin da ya ɗauka tun farko na sauka daga kujerarsa idan tikitin shugaban kasa ya faɗa hannun ɗan arewa.

Gwamna Samuel Ortom.na jihar Benuwai.
Dalilin Da Yasa Shugaban PDP Na Ƙasa Ya Shiga Hatsari, Gwamna Ortom Hoto: Aersaa Peter/facebook
Asali: Facebook

The Nation ta rahoto cewa Ayu ya fito ne daga yankin Jemgbah da ya ƙunshi ƙananan hukumomin Gboko, Tarka, da Buruku yayin da Ortom ya kasance ɗan yankin Minda da ya ƙunshi Makurdi, Guma, da Gwer.

Kara karanta wannan

Asiri Ya Tonu: An Kama Wani Nasiru Idris Ɗauke Da Katin Zabe Sama da 100 a Jihar Sakkwato

Gwamnan ya yi wannan furucin ne cikin harshen Tiv yayin da ya karɓi bakuncin Sarakunan a gidan gwamnati dake Makurdi, babban birnin jihar Benuwai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ƙara da cewa akwai tsarin daidaito a jam'iyyar PDP, idan kujerar shugaban ƙasa na wannan yankin to shugaban jam'iyya na ƙasa zai fito ne daga ɗayan yankin.

Samuel Ortom yace:

"Iyorchia Ayu ya yi alƙawarin zai sauka daga kujerar shugaban jam'iyya idan har tikitin shugaban kasa ya faɗa hannun ɗan arewa amma ya gagara cika alƙawarin. Ana ganin kamar Ortom ke yaƙarsa, ba gaskiya bane."

Mu muka tallafa masa ya zama shugaban PDP - Ortom

A cewar Ortom lokacin da yake faɗi tashin ganin Ayu ya ɗare kujera mafi kololuwa a PDP da yawan mutane sun gargaɗe shi amma ya tsaya tsayin daka.

Ya faɗa wa Sarakunan gargajiyan yankin Jemgbah cewa babu wata matsala tsakaninsa da ɗansu.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Wani Tsohon Gwamna Kuma Babban Jigon PDP Ya Tsame Kansa Daga Kamfen Atiku 2023

Game da Atiku Abubakar, gwamnan yace ɗan takarar shugaban ƙasan ya ci masa mutunci kuma wajibi ne ya hito fili ya nemi afuwa.

A wani labarin kuma Atiku Ya Shilla Kasar Amurka, An Gano Babban Abinda Ya Fitar da Shi Najeriya

Wasu rahotanni sun tabbatar da cewa ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar PDP, Atiku Abubakar, na ƙasar Amurka tun ranar Talata.

Tsohon mataimakin shugaban zai gana da wasu Jami'an gwamnatin Biden domin neman goyon bayansu a 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262