Gwamnan Jihar Abiya Ya Sallami Wasu Daga Cikin Tawagar Hadimansa
- Hadimai, mashawarta da wasu mataimakan kai da kai ga gwamna Okezie Ikpeazu na jihar Abiya sun rasa ayyukansu
- Rahoto ya nuna cewa an sanar da wasu hadiman gwamnan jihar Abiya su tsaya da aikinsu a daren ranar 24 ga watan Oktoba, 2022
- Wannan lamarin dai ya zo da ruɗani da bakon yanayi sakamakon har yanzu gwamnan bai faɗi dalilin korar hadiman ba
Abia - Gwamna Okezie Ikpeazu na jihar Abiya ya rushe tawagar hadimansa na hannun dama da ya ƙunshi mashawarta na musamman, manyan mashawarta da sauransu.
Jaridar Punch ta rahoto cewa matakin gwamnan korar hadiman na kunshe ne a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Sakataren gwamnatin jihar Abiya, Chris Ezem.
Duk da babu wani cikakken bayani kan korar mutanen, sanarwar tace matakin zai fara ne nan take bayan sanar da su ranar 24 ga watan Oktoba, 2022.
Yadda Ortom da Ikpeazu ke wahala saboda tarayya da ni - Wike
Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya yi barazanar fallasa sunayen wasu mutane waɗanda suka shiga suka fita suka hana sakin wasu kuɗin rance daga babban bankin Najeriya (CBN) zuwa jihohin Abiya da Benuwai.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Yace sun yi haka ne domin hukunta gwamna Samuel Ortom da Gwamna Okezie Ikpeazu bisa goyon bayansa kan bukatar shugaban PDP na ƙasa, Iyorchia Ayu, ya yi murabus.
Wike ya yi wannan barazanar ne a wurin bikin karin shekara na gwamna Ikpeazu a mahaifarsa dake ƙauyen Umuobiakwa, ƙaramar hukumar Obingwa, ranar Talata.
Gwamna Wike yace:
"Zan gaya muku yadda wasu kuɗaɗe da ya kamata su dira jihar Abiya domin abokina ya yi amfani da su wajen gudanar ayyukan cigaba suka maƙale sakamakon manakisar wasu dake ganin Ikpeazu baya tare da su."
"Saboda Ikpeazu na goyon bayana, suka je suka dakatar da baiwa jihar Abiya kuɗaɗen da ta tsara zamanantar da Kasuwar Ariara."
A wani labarin kuma Wani Gwamna Ya Jagoranci Dubbanin Mutane Wurin Tattakin Nuna Goyon Baya Ga Tinubu
Gwamnan jihar Osun ya fito ya jagoranci tafiyar kafa ta tsawon kilomita 9.2km a Osogbo domin nuna goyon bayan Tinubu.
Dandazon masoyan APC suka taru a gidan gwamnatin Osun da safiyar nan kafin fara tattakin bayan fitowar gwamna da tawagarsa.
Asali: Legit.ng