2023: Bidiyon Shugaban APC Na Kasa Na Tika Rawa a Wurin Kaddamar da Manufofin Tinubu
- A ranar Juma'a 21 ga Oktoba ne dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya kaddamar da manunofinsa
- A wani bidiyo na ya yadu daga wajen taron, an gano shugaban APC na kasa, Abdullahi Adamu, yana tikar rawar wakar Yarbawa
- Rawar Adamu ya kayatar da shugaban kasa Muhammadu Buhari da sauran manyan jiga-jigan jam'iyya mai mulki da suka taru a wajen
Wani sabon bidiyo na shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Abdullahi Adamu, yana tikar rawa a wajen taro ya yadu.
An gudanar da taron ne don bayyana manufofin dan takarar shugaban kasa na APC, Asiwaju Bola Tinubu da kwamitin yakin neman zabensa, PM News ta rahoto.
A wajen taron, an gano shugaban kasa kasa Muhammadu Buhari, Tinubu, shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan duk a zaune lokacin da Adamu ya bayyana cikin takun rawar wakar yarbawa da ke tashi.
Ya taka rawar har zuwa wajen da shugaban kasa da sauran jiga-jigan jam’iyyar ke zaune sannan ya gaisa da kowannensu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kalli bidiyon a kasa:
Idan Cin Bashi Laifi Ne, Da Yanzu Amurka Ta Zama Magarkama, Inji Tinubu
A gefe guda, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu ya yi watsi da damuwar da 'yan Najeriya ke ciki na bashin da ake bin kasar.
Tinubu ya bayyana cewa, da ace cin bashi laifi ne, da yanzu haka ilahirin kasar Amurka ta zama magarkama saboda tudun bashi, rahoton TheCable.
Tsohon gwamnan na jihar Legas ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a 21 ga watan Oktoba yayin ayyana manufofinsa gabanin babban zaben 2023.
Asali: Legit.ng