Yanzu-Yanzu: Zababben Gwamnan Ekiti Ya Karbi Rantsuwar Kama Aiki
- A yau Lahadi 16 ga watan Oktoba, 2022 aka rantsar da sabon zababben gwamnan jihar Ekiti, Biodun Oyebanji a gaban dandazon mutane
- Manyan kusoshin jam'iyyar APC sun halarci wurin taron ciki har da dan takarar shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
- Gwamna Oyebanji ya karbi mulki hannun tsohon gwamna, Kayode Fayemi, wanda ya rike shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya
Ekiti - Mista Biodun Oyebanji ya karbi shahadar kama aiki a matsayin zababben gwamnan jihar Ekiti na biyar a mulkin demokaraɗiyya.
Oyebanji ya gaji tsohon gwamna, Kayode Fayemi, wanda ya yi aiki a matsayin shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF).
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa an rantsar da Oyebanji tare da mataimakiyarsa, Chief Monisade Afuye, a Ekiti Parapo Pavillon, Ado-Ekiti, babban birnin jihar yau Lahadi, 16 ga watan Oktoba, 2022.
Babban Alkalin jihar Ekiti, Mai shari'a Ayewole Adeyeye, shi ne ya bai wa sabon gwamnan rantsuwar shiga Ofis da misalin karfe 12:52 a gaban dandazon mutane.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Hotunan wurin taron
Manyan jiga-jigan siyasar kasar nan sun halarci wurin taron rantsarwan ciki har da ɗan takarar shugaban ƙasa karkashin inuwar jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu.
A wani labarin kuma Bayan Tawagar Wike, Wasu Gwamnonin PDP Hudu Sun Yi Barazanar Watsi da Atiku a 2023
Rikicin jam'iyyar PDP ya sake ɗaukar sabon babi yayin da wasu gwamnoni hudu suka haɗa kai don yakar Wike da makusantansa.
Gwamnonin sun yi barazanar janye wa daga kamfen Atiku idan har ya rasa mafita kuma ya sa Ayu ya yi murabus.
Asali: Legit.ng