Bayan Tawagar Wike, Wasu Gwamnonin PDP Hudu Sun Yi Barazanar Watsi da Atiku a 2023
- Rikicin jam'iyyar PDP ya sake ɗaukar sabon babi yayin da wasu gwamnoni hudu suka haɗa kai don yakar Wike da makusantansa
- Gwamnonin sun yi barazanar janye wa daga kamfen Atiku idan har ya rasa mafita kuma ya sa Ayu ya yi murabus
- Daga cikin gwamnonin akwai Godwin Obaseki na jihar Edo da Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa
Rikicin cikin gida a jam'iyyar PDP ya buɗe sabon shafi yayin da karin wasu gwamnoni hudu suka yi barazanar kauracewa ɗan takarar shugaban ƙasa, Atiku Abubakar.
A rahoton jaridar The Nation, gwamnonin sun yi barazanar cewa zasu fice daga tawagar kamfen Atiku idan har aka amince da bukatar murabus ɗin shugaban PDP na ƙasa, Iyorchia Ayu.
Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas da 'yan tawagarsa sun bukaci Ayu ya sauka daga mukaminsa a matsayin sharaɗin da zai sa su mara wa takarar Atiku baya a 2023.
A cewar tsagin Wike, babu adalci ko kaɗan ɗan takarar shugaban ƙasa da shugaban jam'iyya na kasa baki ɗaya su fito daga yanki guda.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wata majiya da jaridar ta tattara ta nuna cewa Atiku ya fara saduda kana yana duba yuwuwar biya wa gwamna Wike buƙatarsa.
Sunayen gwamnoni hudu ta suka haɗa kai don yakar Wike
Gwamnonin hudu su ne;
1. Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo
2. Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa
3. Gwamna Duoye Diri na jihar Bayelsa
4. Gwamna Darius Ishaku na jihar Taraba.
Legit.ng Hausa ta fahimci cewa gwamnonin sun samu goyon bayan fitattun jiga-jigan jam'iyyar PDP masu alaƙa da rikicin.
Meyasa ba su kaunar Wike ya cimma burinsa?
Bayanai sun nuna cewa tawagar gwamnonin sun harzuƙa ganin halayyar da Wike ke nuna wa, inda suka ƙara da cewa, "Ya yi mai muninsa."
Haka nan sun nuna damuwar cewa gwamna Wike da magoya bayansa ka iya bijiro da wata sabuwar bukata bayan sun cimma nasara a tsige Ayu daga kujerarsa.
"Bisa la'akari da yadda abun ya ki ƙarewa tsawon lokaci, wasu daga cikin jagororin jam'iyya na ganin bai dace a bar mutum ɗaya ya juya akalar PDP ba don ɗaukar fansa," a cewar wata majiya.
Bayan gwamna Wike, akwai wasu gwamnoni huɗu dake tsaginsa, Seyi Makinde na jihar Oyo, Samuel Ortom na jihar Benuwai, Okezie Ikpeazu na Abiya da Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu.
A wani labarin kuma Lamari Ya Dagule Bayan Atiku Yace Arewa Bata Bukatar Bayerabe Ko Ibo Ya Mulki Najeriya a 2023
Gabannin zaben shugaban kasa na 2023, lamura na kara dagulewa a bangaren dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar.
Atiku ya bayyana cewa yan arewa basa bukatar dan takara Bayarabe ko Ibo ya mulke su a 2023.
Asali: Legit.ng