Ina da Kwarin Guiwar Zan Lashe Zaben Shugaban Kasa a 2023, Tinubu
- Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya bayyana kwarin guiwar da yake da ita ta samun nasara a zaben shugaban kasa na 2023
- Ɗan takarar shugaban kasa a inuwar APC yace zai kafa gwamnati da mutane masu kwarewa don ceto tattalin arzikin Najeriya
- Ya kuma roki gwamnan Kaduna, Malan Nasiru El-Rufai da ya hada hannu da shi don yi wa kasa aiki
Kaduna - Ɗan takarar shugaban ƙasa karkashin inuwar jam'iyyar APC mai mulki, Sanata Bola Ahmed Tinubu, ya nuna kwarin guiwar cewa zai lashe babban zaben 2023 dake tafe.
Tinubu ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi a wurin taron tattalin arziki da zuba hannun jari wanda ya gudana a Kaduna ranar Asabar, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.
Tinubu ya yi alkwarin warware matsalolin da suka addabi ƙasar nan idan yan Najeriya suka amince masa ya zama shugaban ƙasa a zabe mai zuwa. Ya kara da cewa.
"Ina da kwarin guiwar faɗa muku cewa zan ja ragamar ƙasar nan a zaɓen 2023 tare da goyon bayan da zan samu daga wurin ku."
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Ina da basirar magance dukkanin kalubalen da suka hana Najeriya motsi kana daga bisani na dawo da ita kan turba mai kyau."
Tsohon gwamnan jihar Legas ɗin yace zai samar da tsarukan tattalin arziki masu kyau domin saukaka kasuwanci da kuma inganta samar da wutar Lantarki da rarrabata.
"Najeriya zata tsallake zuwa matakin ci gaba, zan haɗa mutane masu kwakwalwa maza da mata domin ci gaban ƙasar mu. Zamu gina gwamnati mai inganci don magance zurarewar kudin shiga."
Ka zo mu haɗa karfi - Tinubu ya roki El-Rufai
Ɗan takarar APC ya roki gwamnan Kaduna, Malam Naairu El-Rufa'i ya haɗa hannu su yi aiki tare idan Allah ya sa aka zaɓe shi shugaban kasa a 2023.
Bugu da ƙari ya roki gwamnan kar ya bar kasar nan a zabe mai zuwa, yana mai cewa, "Sabida muna bukatar basirarka a wannan lokaci mai muhimmanci."
Da yake martani kan rokon Tinubu, Gwamna Malam El-Rufai, yace zai zauna a ƙasar nan ko da kuwa zai rika zuwa ne yana koma wa, PM News ta ruwaito.
A wani labarin kuma Atiku Abubakar ya gana da jagorocin arewa a Kaduna, ya ɗaukar musu muhimman akawurra
Atiku Abubakar ya yi alkawarin magance matsalar tsaro da ya addabi yankin arewa idan ya ɗare shugaban kasa a 2023.
Ɗan takarar kujera lamba ɗaya a inuwar PDP yace ya shirya tsafɓwajen tsamo tattalin arzikin kasar nan daga durkushe wa.
Asali: Legit.ng