Ana Gab da Zaben 2023, Gwamna Wike Ya Nada Sabbin Hadimai 14,000
- Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya nada sabbin hadimai 14,000 a ɓangarori daban-daban na gwamnatin jiharsa
- A wata sanarwa da kakakinsa ya fitar yau Talata, gwamna Wike yace naɗin mutanen zai fara aiki ne nan take
- Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da siyasa ta ɗau zafi a jihar Ribas biyo bayan rattaba hannu kan dokar hana gangamin siyasa
Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya naɗa sabbin mashawarta 14,000 a sassa daban-daban na gwamnatinsa, kamar yadda jaridar This Day ta ruwaito
A wata sanarwa da kakakin gwamnan, Kelvin Ebiri, ya rattaɓa wa hannu, Wike yace sabbin hadiman zasu taka muhimmiyar rawa a gwamnatinsa.
Bugu da kari bayan mashawarta 14,000 da ya naɗa, gwamna Wike ya ƙara naɗa jami'an haɗin guiwar gunduma 319 da kuma wasu 40 na kananan hukumomi.
2023: Sanatan PDP Ya Gargadi Ayu, Atiku Game da Wutar da Ka Iya Tashi Idan Suka Yi Watsi da Gwamnoni 5
Yace naɗin mutanen zai fara aiki ne nan take, sai dai har zuwa yanzu da muƙe haɗa wannan rahoton ba'a bayyan sunayen sabbin hadiman gwamnan ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Legit.ng Hausa ta tattaro cewa na hasashen cewa Wike ya yi waɗannan naɗe-naɗen ne a wasu dabaru na tunkarar babban zaɓen 2023.
Haka zalika, ta wani fannin ana ganin gwamna Wike na kokarin cika alƙawarin da ya ɗauka na cika cikin mutane yayin da wa'adin mulkinsa ke gab da ƙarewa.
A 'yan makonnin nan ruɗani siyasa ya dabaibaiye jihar Ribas, musamman bayan rattaɓa hannun gwamna kan dokar da ta haramta gangamin siyasa a makarantu da sauran wurare ba tare da sahalewar gwamnati ba
Dokar dai ta sha suka daga jam'iyyun siyasa da ƙungiyoyi daban-daban a jihar, wanda a cewar wasu an kirkiro ta ne domin durkusad da tsagin adawa.
ADC Ta Kori Jiga-jiganta a jihar Oyo
A wani labarin kuma Jam'iyyar ADC Ya Kori Tsohuwar Shugabar Majalisar Dokoki da Wasu Jiga-Jigai a Jihar Oyo
Jam'iyyar African Democratic Congress, (ADC) ta kori mace ta farko da ta rike kujerar kakakin majalisar dokokin jihar Oyo , Monsurat Sunmonu.
ADC ta ɗauki matakin korar Monsurat tare da wasu jiga-jigan jam'iyyar.saboda sun goyi bayan tazarcen Seyi Makinde, gwamnan jihar Osun na jam'iyyar PDP.
Asali: Legit.ng