Kamar Zomo Ne Ke Bin Zaki, Al-Mustapha Ya Ce EFCC, ICPC Ba Za Su Iya Yaki da Cin Hanci da Rashawa Ba
- Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar AA ya bayyana cewa, sam Najeriya bata shirya yaki da rashawa ba
- Ya soki yadda hukumar EFCC da ICPC ke tafiyar da lamurransu a kasar tare da cewa sam basu san inda suka dosa ba
- Ya ce kawai a bashi damar mulkar Najeriya, zai tabbatar da komai ya tafi daidai, musamman wajen yaki da rashawa
Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar AA, Hamza Al-Mustapha ya ce hukumomin da aka kirkira a Najeriya domin yakar rashawa ba za su iya yakar rashawan ba.
Da take zantawa da gidan talabijin na Channels a ranar Talata, tsohon hadimin na marigayi Abacha ya ce idan aka zabe a 2023 shi zai inganta hukumomin dake yaki da rashawa a Najeriya.
2023: Ban Taba Satar Ko Sisi Ba, Daidai Da Naira 10, In Ji Dan Takarar Shugaban Kasa Daga Arewacin Najeriya
A cewarsa:
"A Najeriya, na yi imanin cewa, hukumomin da aikinsu na farko shine kula da tsaro, cin hanci da rashawa a Najeriya ba su wadata ba. Suna da kaskanci sosai; basu da tsari mai kyau."
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zomo na bin zaki a dawa
Ya kuma bayyana cewa, daga abubuwan da yake gani kan yadda yaki da rashawa yake a Najeriya, kamar dai zomo ne ke bin zaki a guje a daji.
Ya kuma koka da cewa, abin bakin ciki ne a ce hukumomin yaki da cin hanci da rashawa ba sa hada kai da sauran hukumomin kasashen waje don tsarawa da gano kudaden da aka ketarar daga Najeriya.
Al-Mustapha ya kuma ce, yana da kwarin gwiwa da kwarjinin iya tunkara tare da hukunta kowane dan rashawa ko ma wanene a kasar nan, rahoton TheCable.
Zaben 2023: Ɗan Takarar Shugaban Kasa Na Babban Jam'iyya Ya Bayyana Abu Guda Ɗaya Da Zai Gyara Najeriya
Ya ce:
"Idan kuna maganan kwarjini ne, nagodewa Allah, ba wai ina alfahari bane."
2023: Ban Taba Satar Ko Sisi Ba, Daidai Da Naira 10, In Ji Dan Takarar Shugaban Kasa Daga Arewacin Najeriya
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Action Alliance (AA), Hamza Al-Mustapha ya ce bai taba satar kudi ba ko daukan arzikin kasa, sai dai ya kare dukiyar kasar duk da matsin lamba da wasu suka yi masa.
Al-Mustapha, yayin hira da aka yi da shi a shirin Politcal Paradigm na Channels Television a ranar Talata ya ce:
"Ban da kudi, ban taba satar ko da naira 10 ba. Na kallubalanci gwamnatoci biyu; Na kallubalanci gwamnatin Abdulsalami Abubakar, kuma na kallubalanci gwamnatin (Olusegun) Obasanjo. Sun yi bincike.
Asali: Legit.ng