Dalilai Biyu Ne Suka Ja Ahmad Lawan Ya Rasa Tikitin Takarar Sanata a Yobe
- Bayan kammala rikicin zaben fidda gwanin dan takarar sanata a jam'iyyar APC a jihar Yobe, kotu ta yanke hukunci
- Ahmad Lawan dai ya rasa kujerarsa ta sanata matukar bai daukaka kara ba a nan gaba kadan bayan hukuncin
- Mun kawo muku dalilai da yasa kotu ta duba ta amince da ba Bashir Machina nasarar lashe zaben fidda gwanin sanata
Yobe - Rikicin ko wanene zai zama dan takarar sanatan da hukumar zabe ta INEC ta amince dashi a APC a mazabar Yobe ta Arewa ya kawo karshe, domin an zabi Bashir Machina a matsayin dan takara.
Wata babbar kotun tarayya karkashin jagorancin Fadima Murtala Aminu ta yanke hukunci a yau Laraba 28 ga watan Satumbam inda ta umarci INEC ta amince da Machina a matsayin dan takarar sanatan APC daga Yobe ta Arewa.
Tikitin takarar dai an jima ana kai ruwa rana akansa tsakanin Ahmad Lawan, shugaban majalisar dattawa da Bashir Bachina tun bayan kammala zaben fidda gwanin APC.
Kotu ta yanke hukuncin da ya ba Bashir Machina gaskiya, don haka shi ne dan takara, to amma ta yaya?
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Na farko, a hukuncin da mai sharia Fadima ta yanke a Damaturu, ta ce zaben fidda gwanin da aka yi a jam'iyyar APC ya samar da Machina ne ba Sanata Ahmad Lawan ba, don haka shi ne dan takarar da ya fito ta hanya halastacciya.
Ahmad Lawan bai halarci zaben fidda gwanin sanata ba
Na biyu, ta ta ce kamata ya yi Ahmad Lawan ya halarci zaben fidda gwanin dan takarar sanata, kana ya lashe zabe kafin zama dan takara.
Ta yin karin bayani da cewa, bai halarta ba, don haka tun farko bai ma kamata INEC ta fara duba Ahmad a matsayin dan takara ba.
Hakazalika, kotun ta rushe zaben fidda gwanin da aka sake a jihar Yobe, inda aka samar da Ahmad Lawan a matsayin dan takara a ranar 9 ga watan Yuni.
Idan dai Ahmad Lawan bai daukaka kara ba kuma ya yi nasara a kotun daukaka kara, to ya yi sallama da majalisar dattawa bayan zaben 2023.
Zan Yi Kamfen A ‘Kowane Sashe Na Najeriya’, inji Dan Takarar APC Tinubu
A wani labarin, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana kadan daga shirinsa na kamfen din zaben 2023, Channels Tv ta ruwaito.
Tinubu ya ci alwashin cewa, zai taka kowane bangare a Najeriya domin tallata aniyarsa ta gaje kujerar Buhari a 2023.
A baya an yada jita-jitar cewa, akwai yiwuwar lafiyar Tinubu ta hana shi samun damar yawo a jihohin Najeriya da sunan kamfen.
Asali: Legit.ng