'Dan Hakin da Ka Raina: Kuri'un da Peter Obi Zai Samu Zasu Girgiza 'Yan Siyasa, Peter Ameh
- 'Dan takarar kujerar majalisar wakilai a jam'iyyar LP na mazabar Ankpa, Peter Ameh, ya ce Obi zai bai wa 'yan Najeriya mamaki
- Ya ankarar da manyan 'yan siyasa a fitattun jam'iyyun kasar nan da kada su raina shi don nasararsa zata bada mamaki
- Yace jam'iyyar LP ta taba kawo gwamna daya da 'yan majalisu da yawa, don haka nasarar Peter Obi tabbatacciya ce
Lokoja, Kogi - Manyan 'yan siyasan fitattun jam'iyyu a kasar nan an ankarar da su kan cewa su yi taka-tsan-tsan kuma kada su zuba ido tare da raina 'dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar LP, Peter Obi, jaridar Independent ta rahoto hakan.
'Dan takarar majalisar dattawa na jam'iyyar LP a mazabar Ankpa, Peter Ameh ya sanar da hakan ga manema labarai a wani taro da aka shirya don masu takarar kujerun majalisa na jam'iyyar wanda aka yi a Lokoja dake jihar Kogi.
Ameh ya bayyana cewa, akasin yadda wasu 'yan siyasa suka sakankance na cewa 'dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar LP, Peter Obi, ba shi da tsarin da ya dace yayi nasara a zaben, hakan ba gaskiya bane.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Mai fatan darewa kujerar majalisar wakilan yankinsa a karkashin jam'iyyar LP, yace jam'iyyarsu ta samar da gwamna a wani lokaci da wasu 'yan majalisun tarayya kuma ta jera 'yan takararta da ake fatan su yi nasara a zaben 2023 mai gabatowa.
El-Rufai Ya Girgiza da Jin Abin da Peter Obi Yake Fada Domin Jawo Kuri’un Kiristoci
A wani labari na daban, Ayekooto Akindele ya dauko wani fai-fen bidiyo inda aka ji Peter Obi yana jawabi a coci, ya na nunawa kiristoci cewa su tashi tsaye.
Ayekooto Akindele wanda rikakken masoyin Bola Tinubu da jam’iyyar APC mai mulki ne, ya zargi ‘dan takaran LP da amfani da addini a siyasa.
A wannan gajeren bidiyo da yake yawo a Twitter, Obi ya fadawa mabiya addinin kirista cewa mutanensu ne ‘yan bindiga suke yin gaba da su.
Haka zalika ‘dan siyasar yace daliban da yajin-aikin da ake yi a jami’o’in gwamnati ya shafa, kiristoci ne, amma duk da haka jama’a sun yi gum.
Akindele ya na mai raddi da gatse a shafinsa, ya nuna lamarin rashin tsaro da yajin-aikin da kungiyar ASUU take yi ya shafi Musulmi da Kirista.
Asali: Legit.ng