Atiku Ya Nada Saraki, Shekarau da Wasu Jiga-Jigan PDP a Wasu Muhimman Mukamai

Atiku Ya Nada Saraki, Shekarau da Wasu Jiga-Jigan PDP a Wasu Muhimman Mukamai

  • Mai neman zama shugaban ƙasa a inuwar PDP, Atiku Abubakar, ya sake yin wasu muhimman naɗe-naɗe a tawagarsa
  • Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, da Sanata Ibrahim Shekarau sun samu shiga sabon naɗin Atiku
  • Wannan na zuwa ne kawanki biyu bayan APC ta fitar da tawagar yaƙin neman zaɓen Bola Ahmed Tinubu a 2023

Yayin da ake shirin fara kamfe na zaɓen 2023, mai neman zama shugaban ƙasa a inuwar PDP, Atiku Abubakar, ya yi sabbin naɗe-naɗe masu muhimmanci da nufin karfafa tawagar yaƙin neman zaɓensa.

Channels TV ta ruwaito cewa waɗanda Atiku ya naɗa sun haɗa da, tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, a matsayin wakilin ɗan takarar na musamman da Sanata Pius Anyim, a mukamin mashawarci na musamman.

Kara karanta wannan

Siyasar 2023: Atiku Abubakar Ya Canza Salo, Ya Fara Kulle-Kullen Wargaza Karfin Gwamna Wike

Alhaji Atiku Abubakar.
Atiku Ya Nada Saraki, Shekarau da Wasu Jiga-Jigan PDP a Wasu Muhimman Mukamai Hoto: channelstv
Asali: UGC

Sauran waɗanda suka samu shiga a matsayin mashawarta na musamman sune, tsohon gwamnan Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, tsohon gwamnan Osun, Prince Olagunsoye Oyinlola da kuma Sanata Ehigie Uzamere.

Bugu da ƙari, an naɗa tsohon shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Uche Secondus, a mukamin mashwarci ta fannin fasaha. Naɗe-naɗen zasu fara aiki nan take, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya roki waɗanda Allah ya ba muƙaman su baje kolin kwarewarsu wajen tabbatar da yaƙin neman zaɓen ya haifar da nasara a zaɓen 2023.

APC ta fitar da tawagar kamfen Tinubu

Wannan cigaban na zuwa ne kwanaki biyu kacal bayan jam'iyyar APC mai mulki ta fitar da tawagar yaƙin neman zaben shugaban kasa mai ƙunshe da mambobi 422 tare da ɗora musu nauyin tabbatar da nasarar Bola Tinubu a zaɓen 2023.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa a PDP: Shugaban Yaƙin Neman Zaɓen Atiku Yace Yana Nan Tare da Gwamna Wike

Jerin sunayen mambobin ya ƙunshi tsofaffin ministoci, gwamnoni dake kan madafun iko da wasu jiga-jigai masu faɗa a ji a jam'iyyar APC.

A wani labarin kuma Kwankwaso Ya Mamaye Mahaifar Shugaba Buhari, Ya Baiwa Mutane Mamaki

Mai neman kujerar shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, ya kai ziyara jihar Katsina.

Tsohon gwamnan jihar Kano ya buɗe sabuwar Sakatariyar jam'iyya mai kayan marmari a mahaifar shugaban ƙasa, Daura.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262