Sanata Nnamani Na Jam'iyyar PDP Yana Mana Aiki Ne, APC Ta Magantu

Sanata Nnamani Na Jam'iyyar PDP Yana Mana Aiki Ne, APC Ta Magantu

  • Jam'iyyar APC ta jaddada cewa sunan Sanata Chimaroke Nnamani da aka gani a cikin mambobin Ƙamfen shugaban kasa ba kuskure bane
  • A wata sanarwa da majalisar yaƙin neman zaɓen ta fitar, tace Sanatan, wanda mamba ne a PDP ya zaɓi ya mara wa Tinubu baya
  • Haka nan kuma majalisar da tabbatar wa gwamnoni cewa tana sane da sunayen da suka aike mata kuma kowa zai shiga ciki

Abuja - Majalisar yaƙin neman zaɓen ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC (PCC) ta jaddada cewa sanya sunan Sanata Chimaroke Nnamani a cikin mambobinta 422 ba kuskure bane.

A wata sanarwa da ta fitar a shafinta na Tuwita, majalisar Kamfen tace jerin sunayen na mambobin tawagar yaƙin neman zaɓen da ta fitar a karshen makon nan sahihi ne.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Bayan Mako Guda Amurka, Shugaba Buhari Ya Dawo Nanjeriya, hotunan sun bayyana

Jam'iyyar APC.
Sanata Nnamani Na Jam'iyyar PDP Yana Mana Aiki Ne, APC Ta Magantu Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Sanarwan mai ɗauke da sa hannun Daraktan watsa labarai na PCC, tace mambobin sun kunshi Daraktoci, mataimakansu, da sauran masu ruwa da tsaki.

Meyasa aka sanya mamban PDP?

Da take karin haske kan ganin sunan Sanata Nnamani, Sanata mai ci daga jihar Enugu, PCC ta jaddada cewa ba kuskure bane.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wani sashin sanarwan yace:

"Ya shiga tawagar ne saboda yana da yanci a matsayin mai goyon bayan Asiwaju Bola Ahmed Tinubu. Sanatan wanda yanzu haka baya ƙasa yana Amurka aboki ne na kusa ga Tinubu."
"Ta iya yuwuwa ba inuwar mu ɗaya ba kasancewar sanata ne a inuwar PDP daga mazaɓar Enugu ta gabas amma ganinsa a tawagar Kamfe ta iya yuwuwa ya zaɓi mara wa abokinsa baya ne."

Muna sane da sunayen da kuka aiko mana - PCC ga Gwamnonin APC

Haka nan kuma, tawagar Kamfen ta tabbatar wa gwamnonin jam'iyyar APC cewa ba'a jingine sunayen da suka zaɓo suka aiko don a sanya su cikin mambobi ba.

Kara karanta wannan

Siyasar 2023: Atiku Abubakar Ya Canza Salo, Ya Fara Kulle-Kullen Wargaza Karfin Gwamna Wike

"Wasu sunayen da gwamnonin suka zaɓo an naɗasu cikin jagororin Kamfe yayin da sauran kuma zasu fita a mambobin ɓangarori da dama nan ba ɗa jima wa. Babu sunan da aka bari," inji Sakataren PCC, James Faleke.

A wani labarin kuma kun ji cewa Tinubu Ya Gana da Limaman Kiristoci, Yace Zabar Shettima ba Barazana bace Garesu

Bola Ahmed Tinubu, 'dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar APC ya gana da limaman addinin Kirista na arewacin Najeriya.

Ya bayyanawa manyan limaman cewa, bai zabi Shettima don ware Kirista ba, yayi hakan ne bisa ga cancanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262