Rikicin PDP Ya Kara Tsananta, 'Yan'Yan Jam'iyyar Sun Barke da Zanga-Zangar 'Ayu Must Go' a Katsina
- Matasan PDP a jihar Katsina sun gudanar da zanga-zangar neman shugaban jam'iyyar na kasa, Iyorchia Ayu ya sauka
- Gamayyar kungiyar ta ce ya zama dole Ayu ya cika alkawarinsa na cewa zai yi murabus idan dan arewa ya lashe tikitin jam'iyyar a zaben fidda gwani
- Sun jadadda cewa PDP ba kamfani bane mai zaman kansa don haka dole a tabbatar da adalci ga kowa
Katsina - Gamayyar kungiyar matasan PDP a arewa a sun gudanar da zanga zanga a kofar shiga garin Katsina a ranar Lahadi, suna masu neman Shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Iyorchia Ayu ya sauka.
Fusatattun matasan, wadanda ke dauke da kwaleyen rubutu iri-iri, sun ce lallai sai an cire Ayu daga kujerar mulki kafin zaben 2023.
Sun dauki kwalaye kamar su: 'Dole Ayu yayi murabus’, ‘PDP ba kamfanin mai zaman kansa bane’, Ka cika alkawarinka’, ‘matasan Arewa: mu masu son gaskiya da adalci ne.'
Shugaban gamayyar kungiyar, Shehu Isa Dan’Inna, wanda yayi jawabi ga manema labarai a yayin zanga zangar ya ce dole shugaban jam’iyyar ta PDP na kasa yayi murabus sannan ya daina daukar kansa a matsayin Shugaban jam’iyyar don dakile rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya ce ya kamata Ayu ya cika alkawarin da ya dauka cewa zai yi murabus da zaran an kammala zaben fidda gwanin jam’iyyar idan dan arewa ya zama tsayayyen dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, jaridar Thisday ta rahoto.
Dan’Inna ya ce:
“Muna kira ga shugaban jam’iyyar na kasa da ya cika alkawarinsa. Ayu ya bayyana cewa da zaran an kammala babban taron idan dan arewacin Najeriya ya zama mai rike da tutar PDP zai yi murabus.
“Amma kimanin watanni shida kenan, Ayu bai bar sakatariyar ba, wannan ne dalilin da yasa muke kira ya Ayu a matsayin mai dattako da ya sauka sannan ya daina kiran kansa shugaban PDP na kasa.”
A cewarsa, idan har PDP na son yin nasara a zaben shugaban kasa a 2023, ya zama dole shugaban jam’iyyar na kasa yayi murabus daga kujerarsa kamar yadda yayi alkawari.
Ya yi kira ga kwamitin amintattu, kwamitin NWC da masu ruwa da tsaki a jam’iyyar suyi adalci don kai jam’iyyar ga nasara a 2023.
Rikicin PDP: "Dole Ayu Ya Yi Murabus" Karin Wasu Jiga-Jigai Sun Yaudari Atiku, Sun Koma Bayan Wike
A wani labari makamancin wannan, kungiyar masu ruwa da tsaki na PDP a kudu maso yamma sun ce shugaban jam’iyyar na kasa, Dr Iyorchia Ayu, zai zama jarumi idan yayi murabus da kansa don samun zaman lafiya da nasarar jam’iyyar a zabe.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta tuna cewa jam’iyyar PDP ta fada cikin rikici bayan Alhaji Atiku Abubakar ya zama dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a zaben 2023.
Wasu gwamnonin PDP da jiga-jigan jam’iyyar musamman daga yankin kudancin Najeriya sun ce lallai idan ana son yin adalci babu yadda za a yi yankin arewacin kasar ya rike tikitin shugaban kasa da kuma mukamin shugaban jam’iyya na kasa.
Asali: Legit.ng