Wike Ya Fallasa Ayu, Ya Bayyana Babban Mukamin da Yake So Idan Atiku Ya Ci Zabe
- Nyesom Wike, gwamnan jihar Ribas, ya bayyana cewa Iyorchia Ayu yana hararo kujerar sakataren gwamnatin tarayya idan Atiku ya ci zabe
- Kamar yadda Wike ya fallasa, yace an riga an raba mukamai a karkashin gwamnatin Atiku kuma a sirrance aka yi ba tare da an so su ji ba
- Ya kalubalanci jam'iyyar kan cewa ta dakatar da shi, sun san abinda zai iya kuma su jirace shi idan suka yi hakan
Gwamna Nyesom Wike, a ranar Juma'a, ya sanar da cewa shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Iyorchia Ayu, yana neman mukamin sakataren gwamnatin tarayya idan jam'iyyar ta lashe zaben shugaban kasa a 2023.
A cewarsa, hakan na iya taimaka masa wurin rike mukaminsa na shugaban jam'iyya na kasa da kuma dagewarsa na kada ya sauka daga mukaminsa domin tabbatar da gaskiya da adalci, Punch ta rahoto.
"Idan 'yan Najeriya suka ji abubuwa da yawa da ke faruwa a hanlin yanzu a jam'iyyar da ke son karbar mulki za su matukar girgiza a kai,."
- Wike yace.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kara da cewa:
“A lokacin da muke ta yin magana game da Ayu, alama na nuna cewa mutane ba su san abin da ke ciki ba. Ayu yana so ya kasance a kan mulki. Don ya kasance a can idan PDP ta ci zaben shugaban kasa, yana son a bashi mukamin sakataren gwamnatin tarayya.
"Kun san an raba wadannan mukamai sannan suna son "kananan yara" kamar mu muyi tamkar ba mus an abinda ke faruwa ba
"Zan iya sanar muku hakan saboda yawancin ku ba ku san abin da ke faruwa a cikin jam'iyyar ba. An baiwa wani mukamin shugaban majalisar dattawa. Kuma kuna tsammanin zan zauna a nan a gidan talabijin na kasa in fada muku abubuwan da ban sani ba? Domin sirri ne kawai da wasu abubuwa da ba za mu iya faɗar su a nan ba.”
Da aka tambaye shi game da yiwuwar dakatar da shi kan ayyukan adawa da yaka na jam’iyya, Wike ya ce:
“Wa zai dakatar da ni? Jam'iyyar? Wace jam'iyya? PDP? Babu matsala. Dubi wahala da PDP ke ciki, ba zan hana su, zasu iya.
“Ba wai ina cewa na fi karfin jam’iyya bane. Amma wadanda suka tsere daga jam’iyyar ba za su iya dakatar da ni daga jam’iyyar ba.
"Ina rokon su (PDP) a yau, kada su bata lokaci su ce an dakatar da ni gwamnan Ribas daga jam'aiyyar. Daga nan duk abinda suka gani, zasu dauka. Sun san abinda zan iya yi."
Wike: Yadda Atiku, Saraki, Tambuwal, Aliyu, Suka Ki Amincewa da Rokon Jonathan a 2014
A wani labari na daban, Gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike ya tuno yadda 'dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da tsohon shugaban majalisar dattawa, Saraki suka yi fatali da rokon tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan na hakuri kan hukuncin barin jam’iyyar a 2014.
2023: Gwamnan PDP Mai Karfin Fada A Ji Ya Bayyana Matsayin Jam'iyyar Janyewar Wike Da Mutanensa Daga Takarar Atiku
Jaridar The Nation ta rahoto cewa, Wike ya ce gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tanbuwal yana cikin wadanda suka wulakanta Jonathan bayan taron gangamin 2014 da suka dage kan cewa wannan lokaci ne na arewa.
Asali: Legit.ng