2023: Dole Mu Tabbatar Da Najeriya Kafin Samun Shugaban Kasa, Jonathan

2023: Dole Mu Tabbatar Da Najeriya Kafin Samun Shugaban Kasa, Jonathan

  • Tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, ya gargaɗi yan Najeriya su guji ta da zaune tsaye yayin da ake fuskantar zaɓen 2023
  • Jonathan yace sai Najeriya na doron ƙasa sannan za'a nemi wani muƙami, shugaban kasa, gwamna da sauran su
  • Ya yaba wa matasa bisa fito wa a dama da su a harkokin mulki, inda ya gargaɗe su da su guji kalaman nuna ƙiyayya

Abuja - Yayin da ake tunkarar babban zaɓen 2023, tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya gargaɗi 'yan siyasa da jam'iyyu su guji ta da zaune tsaye, inda yace sai da Najeriya sannan za'a nemi shugaba.

Channels tv tace tsohon shugaban ya yi wannan furucin ne a ranar Talata a Abuja a wurin taron zaman lafiya 2022 da gidauniyar Goodluck Jonathan ta shirya.

Dakta Goodluck Jonathan.
2023: Dole Mu Tabbatar Da Najeriya Kafin Samun Shugaban Kasa, Jonathan Hoto: Channelstv
Asali: Depositphotos

Mista Jonathan ya yi kira ga masu fafutukar ɗarewa madafun iko da su kare martabar ƙasa lamba ɗaya a yawan al'umma a nahiyar Afirka daga rushe wa.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Karɓi Ɗaruruwan Masu Sauya Sheka Daga PDP Zuwa APC Ciki Har da Ɗan Takarar Gwamna

A cewarsa, masu neman zama shugaban kasa, gwamnoni da 'yan majalisu, kowanen su na da rawan da zai iya taka wa wajen inganta demokaraɗiyyar ƙasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Sai ƙasa na nan sannan zamu fara maganar samun shugaba ko gwamna, idan kuka tarwatsa ƙasar, wane shugaban ƙasa kuma zaku bukata?" inji shi.

"Duk wanda ke sha'awar shugabanci tun daga matakin shugaban kasa, gwamna ko Sanata da sauransu, to yana da babban aiki na kare ƙimar ƙasa."
"Baki ɗayan masu neman zama shugaban ƙasa ko gwamna a jihohi da magoya bayansu, abu na farko da ya kamata ku sani shi ne muna bukatar kasancewar ƙasar mu gabanin wanda kuke so ya ɗare madafun iko."

Matasa ku yi takatsantsan - Jonathan

Bugu da ƙari, Jonathan ya yaba wa matasan Najeriya bisa nuna sha'awar shiga a dama da su a zaɓen 2023, inda ya shawarce su da su guji kalaman ƙiyayya a tsakaninsu.

Kara karanta wannan

Abinda Ya Sa Har Yanzu Bamu Magance Ayyukan Ta'addanci Ta Layukan Waya da NIN Ba, Pantami Ya Magantu

Ya ayyana labaran ƙarya, kalaman kiyayya da Farfaganda a matsayin barazana ga demokaraɗiyya, daga bisani ya yi kira ga mazuana ƙasa su guji aikata ɗayansu

A wani labarin kuma Abba Gida Gida Ya Magantu Kan Wani Faifan Bidiyo da Aka Jingina Masa

Abba Gida Gida, mai neman kujerar gwamnan Kano a inuwar NNPP ya nesanta kansa da wani Bidiyo dake yawo a kafafen sada zumunta.

A wata sanarwa da kakakinsa ya fitar, Abba ya nemi ɗaukacin al'umma musamman mambobin NNPP su yi fatali da Bidiyon.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262