2023: Wasu Gwamnonin PDP da Jiga-Jigai Sun Watsar da Atiku, Suna Yi Wa Tinubu Aiki, Majiya
- Alamu sun nuna cewa wasu gwamnonin PDP na shirin yaudarar Atiku Abubakar a zaɓen shugaban kasa na 2023
- Wasu bayanai da aka tattara sun yi ikirarin cewa akwai wasu gwamnoni da jiga-jigan PDP da ka iya koma wa bayan Tinubu na APC
- Ɗaya daga cikin makusanta Atiku ya karyata lamarin, inda a cewarsa babu ƙanshin gaskiya ko kaɗan
Wasu manyan alamu sun nuna cewa ɗan takarar shugaban kasa ƙarƙashin inuwar jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, zai amfama da rikicin da ya ƙi ƙarewa a babbar jam'iyyar hamayya.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa alamun sun nuna wasu gwamnonin PDP da masu faɗa aji sun amince da yi wa ɗan takarar aiki a zaɓen shugaban kasan 2023.
Idan kuna bibiyarmu kun san cewa alaƙa ta yi tsami tsakanin ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar PDP, Atiku Abubakar, da gwamnan Ribas, Nyesom Wike, musamman kan buƙatar Iyorchia Ayu ya yi murabus.
Haka nan gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo, da tsohon mataimakin shugaban PDP na ƙasa, Chief Olabode George, da wasu jiga-jigai sun nemi a tunɓuke shugaban jam'iyya, Mista Ayu, daga kujerarsa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Wannan na zuwa ne a ranar da Tinubu ya naɗa gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu, a matsayin shugaban tawagar yaƙin neman zaɓe a yankin kudu maso yamma.
Wasu Gwamnonin PDP na yi wa Tinubu aiki - Majiya
An tattaro cewa wasu gwamnonin jam'iyyar PDP da masu ruwa da tsaki sun amince zasu mara wa Tinubu baya ba tare da sun fita jam'iyyar ba a zaɓen shekara mai zuwa.
Wasu majiyoyi sun gaya wa Vanguard cewa gwamnonin da wasu jiga-jigai sun sha alwashin goyon bayan takarar Tinubu idan har rikicin jam'iyyar PDP ya ƙi ƙarewa.
Wata majiya mai alaƙa da tafiyar da harkokin APC, ta tabbatar da yuwuwar wannan ƙawance da tsohon gwamnan Legas, tace, "Tabbas dagaske ne."
2023: Babban Cikas, 'Yan Arewa a Jihohi Shida Sun Watsar da Atiku, Sun Faɗi Wanda Suke so Ya Gaji Buhari
"Duba da hanyar da PDP ta ɗakko don magance matsalolinta, ya kamata ku gane ba kowane gwamna zai mara wa Atiku baya ba, abu ne a fayyace da zahirance."
Ba gaskiya bane - Hadimin Atiku
Sai dai wani makusancin tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, wanda ya yi magana da sharaɗin sakaya sunansa, yace lamarin ba gaskiya bane.
"Labarin ba gaskiya bane, babu ƙanshin gaskiya ko kaɗan a wannan lamarin," inji shi.
A wani labarin kuma Matsala ga Atiku, Jigon PDP da Wasu Shugabanni Sun Yi Murabus, Sun Koma APC
Yayin da PDP ke shirin yaƙin neman zaɓen shugaban kasa, a jihar Kebbi jam'iyyar ta gamu da sabon ƙalubalen sauya sheka.
Wani mamba a yankin Danko Wasagu, Hon. Junaidu Wasagu, da shugabannin PDP na gundumomi sun sauya sheka zuwa APC.
Asali: Legit.ng