Janar Buratai Ya Zama ‘Dan Siyasa, Ya Fadi Jam’iyyar Da Za Ta Lashe Zabe a 2023
- An gayyaci Janar Tukur Yusuf Buratai (rtd) domin ya yi jawabi a wajen gangamin matasan APC a Abuja
- Tsohon sojan yace jam’iyyar APC za tayi galaba a 2023, ya yi kira a kaikaice da a zabi Bola Tinubu
- Shi Air Marshal Abubakar Sadique (rtd) wanda ya rike hafsun sojojin sama, ya gabatar da jawabinsa
Abuja - Laftanan Janar Tukur Yusuf Buratai mai ritaya yana ganin nasara tana ga jam’iyyar APC mai mulki a zaben shugaban kasa da za ayi a 2023.
Hukumar dillacin labarai ta fitar da rahoto cewa Janar Tukur Yusuf Buratai (rtd) ya halarci babban gangamin da matasan jam’iyyar APC suke shiryawa.
A jawabin da ya gabatar a ranar Litinin a garin Abuja, tsohon hafsun sojan kasan yace APC tana duk abin da ake bukata yin nasara a zabe mai zuwa.
Tukur Yusuf Buratai ya yi kira ga matasa da su jawo mutane su zabi jam’iyyar APC domin ganin gobensu tayi kyau, sannan a tabbatar da cigaban kasa.
Hudubar Janar Tukur Yusuf Buratai (rtd)
“Dole ku jawo mutane su fito kwansu da kwarkwatarsu domin su zabi ‘dan takaran da ya dace, nayi imani kun san wanda nake nufi.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Idan aka hada da gudumuwar matasa, Jam’iyyar APC ce wanda za ta samu nasara.”
- Janar Tukur Yusuf Buratai (rtd)
Ayi koyi da manyan jiya
Jaridar Vanguard tace tsohon jami’in tsaron ya bada shawara ga matasa da su rika shiga harkar kasa a rika damawa da su, domin su taka rawarsu.
Buratai yake cewa Dr Nnamdi Azikiwe, Tafawa Balewa, Ahmadu Bello da Obafemi Awolowo sun bada gudumuwarsu ne a lokacin suna kuruciya.
Air Marshal Abubakar Sadique
Rahoton da muka samu yace tsohon hafsun sojojin saman Najeriya, Air Marshal Abubakar Sadique ya gabatar da jawabi a wajen taron matasan.
Abubakar Sadique mai takarar gwamnan jihar Bauchi a APC yace jam’iyya mai mulki ba za ta iya rasa zaben 2023 ba, ya yabi wadanda suka shirya taron.
Ganin fiye da 70% na al’ummar Najeriya matasa ne, ana ganin suna da rawar da za su taka a siyasa.
"Peter Obi ba zai iya ba"
An ji labari tsohon gwamnan Edo, Adams Oshiomhole ya yi wa Peter Obi raddi bayan ya yi wata hira da CNN, inda yake bayanin matsalar rashin tsaro.
Oshiomhole wanda ya taba rike shugabancin APC yace Obi ba zai iya inganta tsaron kasar nan ba domin ko da ya yi gwamna a jihar Anambra, ya gaza.
Asali: Legit.ng