Rikicin PDP: Ba'a Yi Wa Gwamna Wike Adalci Ba Kwata-Kwata, Ortom

Rikicin PDP: Ba'a Yi Wa Gwamna Wike Adalci Ba Kwata-Kwata, Ortom

  • Gwamnan jihar Benuwai yace tabbas jam'iyyar PDP ba ya kyauta wa takwaransa na jihar Ribas, Nyesom Wike ba
  • Tun bayan rashin nasara a hannun Atiku a watan Mayu, gwamna Wike ya tsame kansa daga harkokin PDP, lamarin da ya jawo rikici
  • Gwamna Samuel Ortom yace Wike ya tsaya tsayin daka har PDP ta kawo yanzu, don haka tilas a masa adalci

Benue - Gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom, yace jam'iyyar PDP ba ta kyauta wa takwaransa na jihar Ribas, Nyesom Wike, ba.

Gwamna Ortom ya yi wannan furucin ne a wurin taron 'ya'yan PDP da ya gudana ranar Litinin a Makurɗi, babban birnin jihar Benuwai, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Gwamna Wike ya nemi tikitin takara a inuwar PDP a zaɓen fidda ɗan takarar shugaban ƙasa da ya gudana a watan Mayu, amma ya yi rashin nasara a hannun Atiku Abubakar.

Kara karanta wannan

Baya da kura: Atiku Ya Sheka Kasar Waje, Maganar Shawo Kan Rikicin PDP Ya Wargaje

Gwamna Ortom tare da Wike.
Rikicin PDP: Ba'a Yi Wa Gwamna Wike Adalci Ba Kwata-Kwata, Ortom Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Jim kaɗan kafin fara ƙaɗa kuri'a a taron, gwamnan Sakkwato, Aminu Tambuwal, ya janye a dakikar ƙarshe kuma ya umarci magoya bayansa su zaɓi Atiku.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka nan, awanni bayan zaɓen, aka ga shugaban PDP na ƙasa, Iyorchia Ayu, ya garzaya wurin Aminu Tambuwal, inda ya ayyana shi a matsayin, "Gwarzon taron."

Duk bayan haka, Gwamna Wike ya sake rasa tikitin takarar mataimakin shugaban ƙasa bayan Atiku ya zaɓi gwamna Okowa na jihar Delta, ya yi watsi da shawarin kwamiti.

Waɗannan batutuwa da suka taru ne suka haddasa tashin tashina da rikici a babbar jam'iyyar hamayya har ta kai ga mambobin PDP musamman masu goyon bayan Wike na neman Ayu ya yi murabus.

Ya kamata PDP ta yi adalci - Ortom

Da yake jawabi ga masu ruwa da tsaki na jam'iyyar PDP a jihar Benuwai ranar Litinin, gwamna Ortom yace ya kamata a yi wa kowa adalci a jam'iyya.

Kara karanta wannan

Yadda Kwankwaso Zai Lallasa Atiku a Arewa, Ya Ba Da Mamaki a Zaɓen 2023, Tsohon Ɗan Majalisa

"Tunanin a watsar da mutane ba zasu iya komai ba a siyasa haɗari ne saboda ƙuri'a ɗaya tana da matuƙar amfani a siyasance."
"Ba'a yi wa gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas adalci ba, ya zama dole a rarrashe shi a shawo kan lamarin. Wajibi a masa adalci."
"Wike ya tsaya tsayin daka ya goya jam'iyyar nan a bayansa kuma ya kamata a maida hankali kansa."

- Ortom.

A wani labarin kuma Sunayen Tsofaffin Shugabannin Rundunar Soji Uku da Zasu Yi Wa Atiku Kamfe a 2023

Jam'iyyar PDP ta gayyaci tsofaffin Hafsoshin sojin Najeriya su yi wa ɗan takararta na shugaban ƙasa Alhaji Atiku Abubakar, yaƙin neman zaɓe a 2023.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa mutanen uku, Ishaya Bamaiyi, Kenneth Minimah da kuma Martin Luther Agwai, dukkansu Laftanar Janar ne masu ritaya kuma tsofaffin shugabannin hukumar Soji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262