2023: Tabbas Zamu Warware Rikicin Jam'iyyar PDP, Sabon Shugaban BoT

2023: Tabbas Zamu Warware Rikicin Jam'iyyar PDP, Sabon Shugaban BoT

  • Muƙaddaahin shugaban kwamitin amintattu na jam'iyyar PDP, Sanata Wabara, yace tabbas zasu kawo karshen rikicin PDP
  • Yayin ziyarar da suka kai wa gwamna Abiya, Wabara yace zasu yi duk me yuwuwa su tunkari babban zaɓe a inuwa ɗaya
  • Gwamna Ikpeazu, yace tun farko kuskuren PDP ya jefa Najeriya hannun APC har aka shiga wannan yanayin

Abia - Sanata Adolphus Wabara, muƙaddashin shugaban kwamitin amintattu (BoT) a jam'iyyar PDP ya tabbatar da cewa zasu kawo ƙarshen rikicin cikin gida da ya mamaye jam'iyyar.

Daily Trust ta ruwaito cewa Sanata Wabara ya ba da wannnan tabbacin ne yayin da ya jagoranci mambobin BoT suka ziyarci gwamna Okezie Ikpeazu na jihar Abiya a mahaifarsa Umuobiakwa.

Sanata Adolphus Wabara.
2023: Tabbas Zamu Warware Rikicin Jam'iyyar PDP, Sabon Shugaban BoT Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

PDP ta tsinci kanta cikin rikici tun bayan kammala zaɓen fidda gwani a watan Mayu, wanda ya ayyana tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, a matsayin ɗan takara a 2023.

Kara karanta wannan

2023: Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa, Rabiu Kwankwaso, Ya Yi Kus-Kus da Wani Gwamnan APC

A halin yanzu, Sanata Wabara yace zasu yi iya bakin kokarinsu don tabbatar da an lalubo ƙullin da kuma warware rikicin gabanin babban zaɓen 2023 da ke tafe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bugu da ƙari, Yace kwamitin amintattu zai ziyarci gwamnoni da masu ruwa a tsaki da nufin dawo da zaman lafiyar da aka rasa a jam'iyyar PDP, vanguard ta ruwaito.

Kazalika, Wabara ya misalta gwamna Ikpeazu da mutum mai daraja wanda ake ganin girmansa a jam'iyya, inda ya kara da cewa ba za'a iya shafe gudummuwar da ya bayar ba wajen gina PDP.

Dole a nemi masalaha - Ikpeazu

Da yake nasa jawabin, gwamna Ikpeazu yace akwai buƙatar a zauna a nemo hanyar sulhu idan har dagaske ana son jam'iyyar ta kai labari a zaɓen 2023.

Yace akwai bukatar PDP ta sake nazari kan abubuwan da suka faru a baya-bayan nan don kauce wa faɗa wa gidan jiya abinda ya auku a zaɓen 2015.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu Ya Shiryawa su Atiku, An Kafa Kwamitocin da Za Su Taimaka Masa a Kudu

"Kuskuren mu ne ya kai ƙasar mu cikin wannan halin da take ciki a yanzu, ba don haka ba ai ba zamu faɗa hannun jam'iyyar APC ba."

A wani labarin kuma Ɗan Takarar Gwamna, Sakataren Jiha da Wasu Jiga-Jigai Sun Fice Daga Jam'iyyar PDP a Jihar Arewa

Alhaji Abba Gana Tata, ya sanar da jagororin PDP a jihar Yobe cewa daga ranar 13 ga Satumba, 2022, ya fice daga jam'iyyar baki ɗaya.

Sakataren PDP na jihar Yobe, da wasu shugabannin a mataki daban-daban sun bi sahun Abba Gana sun fice daga jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262