Tinubu Ya Samu Gagarumin Goyon Baya Daga Wani Shahararren Malamin Addini, Ya Ce Shine Zai Gyara Najeriya
- Gabannin babban zaben 2023, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya samu goyon baya daga wani malamin addini
- Fasto John Desmond wanda ya kasance shugaban kungiyar YPN, ya bayyana cewa Tinubu na da abubuwan da ake bukata a wajen shugaba don kawo canji
- Ya bukaci yan Najeriya da su zabi tsohon gwamnan na jihar Lagas domin shi zai iya gyara Najeriya
Shugaban kungiyar Young Professionals of Nigeria (YPN), Fasto John Desmond, ya nuna goyon bayansa ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Desmond ya yi kira ga yan Najeriya da su zabi Tinubu a matsayin shugaban kasa a babban zaben 2023 mai zuwa.
Ya yi kiran ne Umuahia, jihar Abia, yayin wani rangadi na wayar da kan matasan kungiyar YPN wadanda suke mambobin APC a fadin kudu maso gabas, jaridar The Nation ta rahoto.
Tinubu Zai Gyara Najeriya, In ji Desmond
Malamin addinin ya kuma bayyana cewa Tinubu na da karfin gwiwa, hangen nesa da karfin gyara Najeriya.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Rahoton ya nakalto Desmond yana cewa:
“Tinubu mutum ne da bai da son kai da tarin nasarori. Ya kasance dan siyasa, dan kasuwa kuma jagora mai tunani wanda ya samu babban gurbi a tarihin Najeriya a matsayin daya daga cikin manyan shugabannin siyasa da suka kawo gagarumin sauyi ta fuskacin damokradiyya a siyasar kasar.
“Jagaban ya fahimci amfanin matasa a Najeriya. Ya hango karfin wannan sashe namu kuma ya gaggauta amfani da shi.
“Sakamakon wannan yunkuri shi ne billowar jiga-jigan siyasa matasa kamar su, Raji Fashola, Yemi Osinbajo, Akinwumu Ambode, Banire, Obanikoro, Alake, Fayemi, Edun, Aregbesola, Akabueze, Igbokwe, Fowler, da sauransu."
Rashin Lafiya: "Ba Kan Tinubu Farau Ba Kowa Da Matsalar Shi", Jigon APC Ya Yi Martani Mai Zafi
A wani labarin, wani jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Prince Tajudeen Olusi, ya gargadi masu zolayar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Asiwaju Bola Tinubu, kan lafiyarsa.
Olusi ya bayyana cewa babu wani dan adam da baya da wata matsala ta rashin lafiya da ke damunsa a rayuwa.
Da yake jawabi a wata hira da jaridar Daily Independent a ranar Talata, Olusi, ya ce duba da yadda Tinubu ke yawo a fadin kasar tun bayan da ya lashe tikitin APC ba tare da ya kwanta ba ya nuna babu abun da ya samu lafiyarsa.
Asali: Legit.ng