Tsohon Ɗan Takarar Gwamna a Jihar Ya Fice Daga PDP, Yana Shirin Shiga APC

Tsohon Ɗan Takarar Gwamna a Jihar Ya Fice Daga PDP, Yana Shirin Shiga APC

  • Tsohon ɗan takarar gwamna a jihar Yobe karƙashin PDP ya tsame jikinsa daga harkokin jam'iyyar, ya sanar da yin murabus
  • Alhaji Abba Gana Tata, ya sanar da jagororin PDP a jihar Yobe cewa daga ranar 13 ga Satumba, 2022, ya fice daga jam'iyyar baki ɗaya
  • Sakataren PDP na jihar Yobe, da wasu shugabannin a mataki daban-daban sun bi sahun Abba Gana sun fice daga jam'iyyar

Yobe - Tsohon ɗan takarar gwamna karkashin inuwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Yobe, Alhaji Abba Gana Tata, ya fice daga jam'iyyar ana shirin tunkarar babban zaɓen 2023.

Alhaji Tata ya bayyana matakin da ya ɗauka ne a wata wasika da ya aike ɗauke da adireshin shugaban PDP a ƙaramar hukumar Bursari da shugaban jam'iyya na jiha, Ambasada Umar El-Gadh.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Atiku ya sake kai ziyara jihar Kudu, ya samu tarbar gwamna Makinde

Sauya sheƙa a siyasar Najeriya.
Tsohon Ɗan Takarar Gwamna a Jihar Ya Fice Daga PDP, Yana Shirin Shiga APC Hoto: Yunus Boska/Facebook
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta ci karo da kwafin wasiƙar tsohon ɗan takarar gwamnan, wanda wani sashinta yace:

"Na rubuta wannan takarda ne domin na sanar a hukumance cewa na yanke yin murabus daga kasancewa mamban jam'iyyar PDP."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Ina mai sanar muku da cewa na bar PDP daga ranar Talata 13 ga watan Satumba, 2022, ga katina nan na haɗo muku da shi mai lamba No. 1533599."

Na tsame kaina daga dukkan wasu harkokin PDP

Legit.ng Hausa ta gano cewa Alhaji Gana Tata ya sanar da jagorocin PDP a wasikar murabus ɗinsa cewa daga ranar Talata ya raba gari da jam'iyyarsu a matakin gundunma, ƙaramar hukuma da jiha.

Ya ci gaba da cewa:

"Na sanar da shugaban jam'iyya a gundumar Musaba, ƙaramar hukumar Bursari da shugaban PDP na jihar Yobe wannan matakin kuma zai fara aiki ne nan take daga ranar 13 ga Satumba."

Kara karanta wannan

2023: Atiku Ya Shiga Wata Matsala, Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Ya Koma Bayan Gwamna Wike

"Saboda haka daga lokacin da takarda ta ta riske ku ina mai gaya muku cewa na tsame kaina daga dukkan wasu harkokin jam'iyyar PDP tun daga matakin gunduma, ƙaramar hukuma, jiha da ƙasa baki ɗaya."

Wasu shugabannin PDP a Yobe sun bi sahunsa

A wasu takardun ficewa daga PDP da aka aike wa wakilin Legit.ng Hausa, jam'iyyar adawa ya rasa manyan jiga-jiganta a jihar Yobe sakamakon fitar Alhaji Abba Gana.

Sakataren jam'iyyar na jiha, Sani Bilal Ahmed Lawan, shugaban PDP a ƙaramar hukumar Bursari, shugaban matasa da wasu tsaffin shugabanni sun tabbatar da ficewarsu daga PDP a wasiku daban-daban da suka aike wa Ambasada Umar Elgash.

Takardun fita daga PDP a Yobe.
Tsohon Ɗan Takarar Gwamna a Jihar Ya Fice Daga PDP, Yana Shirin Shiga APC Hoto: Yunus Boska/facebook
Asali: Facebook

Mai taimaka wa Abba Gana Tata ta ɓangaren Midiya, Yunus Boska, ya shaida wa Legit.ng Hausa cewa sun yanke barin PDP ne saboda an jingine su a tafiyar da harkokin jam'iyya.

"Ba zaman lafiya a cikin PDP reshen Yobe, ga kiyayya shiyasa muka yanke tattara wa muka fita. Har yanzun bamu yanke jam'iyyar da zamu koma ba sai zuwa gaba kaɗan," inji shi.

Kara karanta wannan

Bayan Karban Dubbannin Masu Sauya Sheƙa, Ɗan Takarar PDP Yace Zaɓen Jam'iyyarsa a 2023 'Jihadi Ne'

Boska ya ƙara da cewa tsohuwar jam'iyyarsu PDP babu shugabanci kuma ba zata kai labari ba a haka a zaɓen 2023 dake tafe.

A wani labarin kuma Wani Jigo An Fallasa Yadda Mambobin APC, PDP Zasu Watsar da Atiku da Tinubu, Su Zaɓi Wani Ɗan Takara a 2023

Jigon jam'iyyar Labour Party, Victor Umeh, yace akwai wasu mambobin APC da PDP da zasu zaɓi Peter Obi a zaɓen 2023.

Umeh, wanda ke neman kujerar Sanata daga jihar Anambra, yace mutane sun gano cewa LP ce kaɗai zata iya ceto Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262