Jam'iyyar APC Ta Kori Shugaban Matasa Kan Wata Sanata Ta Koma PDP
- Shugaban matasan APC reshen jihar Anambra, Innocent Nwanwa, ya rasa mukaminsa bayan sauya shekar Sanata Oduah
- Da yake jawabi ga manema labarai, Mista Nwanwa yace tuni da aike da ƙorafi ga uwar jam'iyya ta ƙasa, Abuja
- Tsohon shugaban matasan ya kasance ɗan amutun Sanata Stella Oduah, wacce ta sauya sheka zuwa PDP
Anambra - Jam'iyyar All Progressive Congress (APC) reshen jihar Anambra ta tsige shugaban matasa na jiha, Innocent Nwanwa.
Nwanwa, ɗan gani kashenin tsohuwar ministar sufurin jiragen sama kuma Sanatan Anambra ta arewa, Stella Oduah, wacce ta sauya sheƙa daga APC zuwa PDP.
Punch ta rahoto cewa Wata majiya ta bayyana cewa mai yuwuwa sauya sheƙar Oduah ta janyo APC ta ɗauki wannan matakin kan shugaban matasa.
Oduah ta shiga jam'iyyar APC ne ana gab da gwabza zaɓen gwamnan jihar Anambra 2021, amma wani lamari tamkar almara, Sanatan ta koma PDP inda ta lashe tikitin takarar Sanata a 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon shugaban matasan, wanda ya yi hira da yan jarida a Awka ranar Lahadi, ya tabbatar da cewa APC ta tsige shi daga matsayinsa da ya lashe a taron jam'iyya na watan Janairu.
Wane mataki ya ɗauka?
Sakamakon haka, Mista Nwanwa ya ce ya rubuta korafi ga uwar jam'iyya ta ƙasa domin ta shiga tsakani kan abin da ya kira, "Rashin Adalci" da aka masa.
Ya yi bayanin cewa bai kamata a hukuntashi saboda uwar gidansa ta sauya sheka zuwa wata jam'iyya. A takardar korafinsa yace:
"Ni, Hon Innocent Nwanwa, an zaɓe ni a matsayin shugaban matasan APC na jiha a wurin taron da ya gudana ranar 30 ga watan Janairu, 2022, kuma aka rantsar da mu a Sakatariya, Amenyi Awka."
"Gaskiya ne na shigo APC tare da Sanata Stella Oduah, amma tun bayan wannan lokacin na kasance mai halartar duk wasu harkokin jam'iyya duk da nasan Sanatar ta sauya sheka."
"Amma abun takaici da bakin ciki shugaban jam'iyya na jiha, Chief Basil Ejidike, ya yi watsi da ni tare da barazanar sauke ni. An daina kira na tarukan shugabanni da harkokin jam'iyya, ya maye gurbi na da wani Jideofor Ejimofor."
Daga karshe ya roki shugaban APC na ƙasa ya yi amfani da ƙarfin ikonsa wajen gyara ɓarnar da aka yi ba kan ƙa'ida ba domin jam'iyya ta samu damar tunkarar 2023.
A wani labarin kuma Atiku Abubakar Ya Rubuta Wasika Ga Yan Najeriya, Yace Zaɓi Biyu Mutane ke da shi a 2023
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya ankarar da yan Najeriya kan zaɓi biyu da suke da shi a 2023.
Atiku, mai neman kujerar shugaban kasa a inuwar PDP, yace 'yan Najeriya zasu tantance tsakanin yanci da azaba.
Asali: Legit.ng