Kano: 'Yan Sanda Sun Damke Jiga-jigan PDP 2 Kan Zargin Zugawa Abacha Karya
- 'Yan sandan jihar Kano sun kama tare da gurfanar da shugaban jam'iyyar PDP na Fagge tare da sakataren jam'iyyar a gaban kotu
- Ana zargins'u da zabga karya tare da hada kai wurin aikata laifi inda suka ce basu bai wa Abacha katin shaidar zama 'dan jam'iyyar PDP ba bayan da kansu suka bada
- A cewar tuhumar, zun yi karya tare da ranstuwa a gabn kotu wanda sun san hakan na iya tada zaune tsaye a jam'iyyar
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Kano - Fannin bincike manyan laifuka na rundunar 'yan sandan Najerya na Zone One dake Kano, ta aike shugaban PDP na karamar hukumar Fagge, Muhammad Auwal da sakataren jam'iyyar, Umar Alhassan kan zargin zagi da Umar Alhassan kan zargin kazafi da suka yi wa Muhammad Sani Abacha, jaridar Vanguard ta rahoto.
Rahoton farko da aka mika gaban babbar kotun tarayya dake Kano yayin gurfanar da jiga-jigan jam'iyyar PDP a wasikar koke da aka mikawa sifeta janar na 'yan sandan Najeriya kuma aka kai wa 'yan sandan Zone one domin bincike, tace bincike ya nuna mutum biyu da suka yi wa Muhammad Sani abacha karya tare da hada kai wurin aikata laifin.
Kamar yadda FIR yace, bayan bincike an gano cewa kusan watanni shida da suka gabata kafin zaben fidda gwanin 'dan takarar gwamnan PDP a Kano, an bai wa Muhammad Sani Abacha katin shaidar zama 'dan jam'iyyar a gundumar Fagge B wanda Muhammad Auwal da Umar Alhassan suka saka hannu.
Kamar yadda rahoton farko na 'yan sandan yace, katin shaidar ne ya tabbatar da cewa Muhammad Abacha 'dan jam'iyyar ne a gundumar Fagge B dake karamar hukumar Fagge.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
“Sai dai, banyan Muhammad Abacha ya ci zaben fidda gwanin na kujerar gwamnan Kano a PDP, kun hada kai tare da karya inda kuka yi rantsuwa a gaban babbar kotun tarayya, inda kuka ce Muhammad Abacha ba 'dan jam'iyyar bane kuma ba a bashi katin shaidar zama 'dan jam'iyya ba, lamarin da kun san karya ne kuma zai iya tada zaune tsaye."
"A don haka ake gurfanar da ku saboda wadannan laifukan da suka yi karantsaye da sashi na 97, 158 da 114 na dokokin Prnal Code."
- 'Yan sandan suka ce.
Jam'iyyar APC Ta Kori Shugaban Matasa Kan Wata Sanata Ta Koma PDP
A wani labari na daban, jam'iyyar All Progressive Congress (APC) reshen jihar Anambra ta tsige shugaban matasa na jiha, Innocent Nwanwa.
Nwanwa, ɗan gani kashenin tsohuwar ministar sufurin jiragen sama kuma Sanatan Anambra ta arewa, Stella Oduah, wacce ta sauya sheƙa daga APC zuwa PDP.
Punch ta rahoto cewa Wata majiya ta bayyana cewa mai yuwuwa sauya sheƙar Oduah ta janyo APC ta ɗauki wannan matakin kan shugaban matasa.
Asali: Legit.ng