Zaɓen 2023 Tamkar Tsakanin Yanci Ne da Azaba, Ya rage Wa Mutane, Atiku
- Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya ankarar da yan Najeriya kan zaɓi biyu da suke da shi a 2023
- Atiku, mai neman kujerar shugaban kasa a inuwar PDP, yace 'yan Najeriya zasu tantance tsakanin yanci da azaba
- Wannan na zuwa ne a lokacin da ya rage yan kwanaki a kaɗa gangar yaƙin neman zaɓen shugaban kasa
Abuja - Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban kasa a inuwar PDP yace babban zaɓen 2023 ba kaɗa kuri'a bane kaɗai, zaɓi ne tsakanin yanci daga kamun kukun da APC ta yi ko azaɓar da Najeriya ke karɓa daga hannunta.
Vanguard ta rahoto Atiku na cewa lokacin fara tallata hajar 'yan takara ya tunkaro don haka akwai bukatar yan Najeriya su tuna abinda ke gaban su.
Tsohon mataimakin shugaban kasa ya yi wannan furucin ne a wata wasiƙar kai da kai ta musamman da ya rubuta zuwa ga 'yan Najeriya ranar Lahadi, 11 ga watan Satumba, 2022.
Ya ƙara da bayanin cewa tunda Agogon Kamfe na gab da fara kyasta wa, "Yana da kyau mu yi amfani da sauran kwanakin da suka rage wajen shiri da gano ƙarfin mu a runfunan zaɓe 176,846."
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Na san cewa ba abu ne mai sauki ba amma zai zama abu mafi muni a bar jam'iyyar APC ta ƙara kwana ɗaya a gadon mulki bayan ranar 29 ga watan Mayu. Zaɓe ya tunkaro mu, zaɓi ne tsakanin kyaun Najeriya da gaza cika alkawarin APC."
"Zaɓe ne tsakanin yanci da azaba kuma ina da yaƙinin cewa zaku yi duk me yuwuwa wajen tabbatar da Najeriya ta tsira daga wahalhalun nan. Ku jawo abokanku su zama masu sa iso a kowace rumfa."
"Mu haɗa karfi da karfe wajen ceto Najeriya, a matsayin tsintsiya ɗaya zamu kai ga nasara."
Zamu kawo karshen rikicin PDP - Atiku
A wani labarin kuma Atiku Abubakar ya faɗi hanya ɗaya da ta dace su bi wajen shawo kan rikitin da hana PDP rawar gaban hantsi
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya ce zasu bi hanya ɗaya domin warware rikicin da ya addabi jam'iyyar PDP.
Ɗan takarar ya kuma sha alwashin cewa zai baiwa mara ɗa kunya idan har ya zama shugaban Najeriya a zaben 2023.
Asali: Legit.ng