Rikitin PDP: Atiku Ya Gana da Yan Takarar Shugaban Kasa, Wike da Wasu Biyu Ba Su Halarta Ba

Rikitin PDP: Atiku Ya Gana da Yan Takarar Shugaban Kasa, Wike da Wasu Biyu Ba Su Halarta Ba

  • Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya gana da yan takarar kudu da suka fafata da zaben fidda gwani
  • Taron wanda ya gudana a gidan Atiku dake Asokoro, Abuja, Wike da wasu yan takara biyu ba su halarci taron ba
  • Tun bayan kammala zaben fidda gwani a watan Mayu, rikici ya raba Atiku da gwamna Wike na jihar Ribas

Abuja - Ɗan takarar shugaban kasa karkashin inuwar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya gana da 'yan takarar da suka fafata a zaɓen fidda gwani, waɗan da suka fito daga yankin kudu, a gidansa dake Asokoro, Abuja.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa kamar yadda aka yi tsammani, Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ɗaya daga cikin yan takarar, bai halarci taron ba wanda ya gudana yau Laraba.

Taron Atiku da yan takarar shugaban kasa.
Rikitin PDP: Atiku Ya Gana da Yan Takarar Shugaban Kasa, Wike da Wasu Biyu Ba Su Halarta Ba Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Sai dai a ruwayar Daily Trust, ba Wike ne kaɗai bai halarta ba, tsohon shugaban majalisar dattawa, Pius Anyim, da gwamnan Akwa Ibom, Udom Emmanuel, duk an neme su an rasa a wurin taron.

Kara karanta wannan

Hotuna: Lamiɗo, Da Wasu Yan Takarar Gwamna 16 Na Jam'iyar PDP Sun Sa Labule da Wike

Su wa suka halarci taron da Atiku?

Daga cikin waɗanda suka hallara, sun haɗa da Dele Momodu, Tari Oliver, Charles Ugwu da kuma Kalu Chikwendu. Daga arewa kuma Muhammed Hayatu-Deen ya samu halarta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin ganawar, Atiku ya yaba wa wadanda suka hallara bisa ɗaukar kaddara da sakamakon babban taro na ƙasa wanda ya ayyana shi a matsayin wanda zai kare tutar PDP a zaben 2023.

Ya kuma ɗauki alƙwarin jawo su a jiki su yi aiki tare gabanin zaɓe mai zuwa, inda ya ƙara da cewa kowane ɗaya daga cikinsu yana da rawar da zai taka a Kamfe.

Yadda Zaɓen fidda gwanin PDP ya kasance

A zaben fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP wanda ya gudana a watan Mayu, Atiku ya tashi da kuri'u 371 inda ya lallasa abokin hamayya na kusa, Wike, wanda ya samu kuri'u 237.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Atiku Abubakar da Gwamna Wike Sun Amince da Bukata Ɗaya Kafin Fara Kamfen 2023

Tun bayan sanar da sakamakon zaɓen Gwamna Wike ya fara taƙun saƙa da Atiku kan zaƙulo gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta a matsayin ɗan takarar mataimaki.

A wani labarin kuma Jam'iyya TaTsige Shugabanninta Na Jihohi 17 Kan Zargin Cin Amana

Jam'iyyar ADC ta ƙasa ta sanar da sauke shugabanninta na jihohi 17 daga kan kujerunsu tare da korar wasu daga jam'iyya.

A wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun shugaba da Sakatare na ƙasa, ADC ta naɗa sabon shugaban kwamitin amintattu (BoT).

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262