Jam'iyyar ADC Ta Tsige Shugabanninta Na Jihohi 17, Na Nada Shugaban BoT
- Jam'iyyar ADC ta ƙasa ta sanar da sauke shugabanninta na jihohi 17 daga kan kujerunsu tare da korar wasu daga jam'iyya
- A wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun shugaba da Sakatare na ƙasa, ADC ta naɗa sabon shugaban kwamitin amintattu (BoT)
- Ta ɗauki wannan matakin ne bayan gano wasu na yi wa jam'iyya zagon ƙasa yayin da take shirin tunkarar 2023
Abuja - Jam'iyyar African Democratic Congress (ADC), ta naɗa Mani Ahmed, wanda ya nemi kujerar shugaban kasa a 2015, a matsayin shugaban kwamitin amintattu (BoT), kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da shugaban ADC na ƙasa, Ralph Nwosu, da Sakatare, Said Abdullahi, suka rattaɓa wa hannu aka raba wa manema labarai ranar Laraba a Abuja.
Sanarwan ta bayyana cewa Ahmed ya zama shugaban kwamitin BoT ne bayan kammala taron gaggawa da kwamitin gudanarwa (NWC) ya gudanar da masu ruwa da tsaki ranar Talata.
A cikin sanarwan, jam'iyyar ADC ta dakatar da Ibrahim Manzo, tsohon mataimakin shugaba na shiyyar Arewa maso Yamma, sannan kuma ta tsige shugabannin jam'iyya na jihohi 17.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A cewar jam'iyyar ta ɗauki wannan mataki a kansu ne bisa zargin yi wa ADC zagon ƙasa da kokarin wargaza jam'iyyar baki ɗaya, Sahara Reporters ta ruwaito
Sanarwan ta ƙara da bayanin cewa waɗannan ayyukan laifin da suka aikata ya saɓa wa sashi na 15 dake ƙunshe a kundin tsarin mulkin jam'iyyar ADC.
"Mun kori tsohon shugaban ADC reshen jihar Abiya. Zamu sanar da waɗanda zasu maye gurbin shugabannin jihohin da aka tunɓuke nan ba da jima wa ba," inji Sanarwan.
Wane mataki ADC zata ɗauka na gaba?
Bugu da ƙari, sanarwan ta roki shugagannin ADC a matakin gundumomi da ƙananan hukumomi da jihohi da su cigaba da aikin sake fasalin jam'iyya domin fara kamfe gadan-gadan.
Ta kuma ƙara wa yan takara na dukkan matakai kwarin guiwar kada guiwowinsu su yi sanyi ganin abubuwan da wasu suka aikata, amma su ɗaura ɗamarar tunkarar babban zaɓen 2023.
A wani labarin kuma Daga Karshe, An Warware Saɓanin Dake Tsakanin Atiku da Wike, Ɗan Takarar PDP Ya Faɗi Abinda Ya Rage
Ɗan takarar kujerar gwamnan Kaduna a inuwar PDP, Isah Ashiru Kudan, yace sun yi nasarar warware saɓanin Atiku da Wike.
A jiya ne, Ashiru da takwarorinsa masu neman kujerar gwamna a jihohi 16 suka ziyarci gwamna Wike na Ribas kan rikicin PDP.
Asali: Legit.ng