2023: Atiku Zai Gana Da Tsofaffin Yan Takarar Shugaban Kasa Na PDP Yau
- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, zai gana da ƴan takarar da suka fafata a zaɓen fidda ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP yau
- Wannan taron zai gudana ne ƙasa da awanni 24 bayan Atiku ya tattauna da tsofaffin mambobin majalisar wakilai na PDP
- A ranar 28 ga watan Satumba, za'a fara yakin neman zaɓe, kuma ana ganin tarukan na da alaƙa da shirin kamfe
Abuja - Mai rike da tikitin takarar shugaban kasa a inuwar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, zai gana da abokan fafatawarsa a zaɓen fidda gwani yau a birnin tarayya Abuja.
Jaridar Tribune ta tataro cewa wasu majiyoyin sun ce an shirya taron ne a kokarin ɗinke barakatar da ta biyo bayan zaɓen fidda gwanin da lalubo hanyar masalaha domin tunkarar gaba.
Ɗaya daga cikin 'yan takarar da suka nemi tikitin kujerar shugaban kasa a PDP (An ɓoye sunansa), wanda ya ba da labarin taron, bai yi ƙarin haske game da batutuwan da zasu baje a teburi yayin zaman ba.
Majiyar ta nuna damuwa kan dambarwar da ta ƙi ƙarewa tsawon lokacin tun bayan kammala zaɓen fidda gwani a watan Mayu da kuma zaɓen abokin takarar Atiku.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Lamarin na ƙara dagulewa duk kuwa da yunkurin ɓangarorin masu faɗa a ji na PDP domin ganin sun sasanta tsagin Atiku da kuma gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas.
Legit.ng Hausa ta fahimci cewa taron na zuwa ne ƙasa da awanni 24 bayan tsohon mataimakin shugaban ƙasan, ya gana da tsofaffin mambobin majalisar wakilai bisa jagorancin tsohon mataimakin kakaki, Emeka Ihedioha a Abuja.
Haka zalika ranar Asabar da ta shuɗe, Atiku ya gana da yan takarar gwamna daga baki ɗaya jihohin Najeiya, duk a wata hoɓɓasa da yake domin shirya wa zuwan lokacin Kamfe ranar 28 ga watan Satumba, 2022.
Wane hali ake ciki tsakanin Atiku da Wike?
A wani labarin kuma kun ji cewa Atiku Abubakar da Gwamna Wike Sun Amince da Bukata Ɗaya Kafin Fara Kamfen 2023
Za'a sake zaman sulhu don kawo karshen rikicin dake tsakanin Atiku Abubakar da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike.
Bayanai sun nuna cewa tuni jiga-jigan biyu suka zaɓi ranar da zasu zauna tattauna wa Ido da Ido gabanin fara kamfe.
Asali: Legit.ng