Jam'iyyar APC a Jihar Adamawa Ta Tsige Shugaba Daga Kujerarsa
- Rikicin jam'iyyar APC a jihar Adamawa ya ƙara tsanani, kwamitin zartarwa ya tsige shugaban jam'iyya, Ibrahim Bilal
- Mai magana da yawun APC-Adamawa, Muhammed Abdullahi, yace sun ɗauki matakin ne kan zargin cin amana da karkatar da kuɗaɗe
- Tuni kwamitin ya maye gurbinsa da mataimakin shugaba, Ismaila Tadawus, bayan mambobi 24 cikin 36 sun sa hannu
Adamawa - Kwamitin zartarwa na jam'iyyar APC a jihar Adamawa ya tsige shugaban jam'iyya, Ibrahim Bilal, daga kujerarsa kan zargin cin amana, sama da faɗi da kuɗaɗe da ƙarya dokokin kwansutushin.
Daily Trust ta ruwaito cewa bayan tsige Bilal, an rantsar da mataimakinsa, Ismaila Tadawus, a matsayin sabon shugaban APC-Adamawa tare da sa hannun Ofisoshi 24 cikin 36.
Kwamitin zartarwan, a wani taro da ya gudana a Sakataryar jam'iyya dake Yola ranar Litinin, ya zargi tsohon shugaban APC a jihar da amfani ƙarfinsa wajen kwashe kuɗaɗe.
A jawabin da ya karanta, kakakin APC, Muhammed Abdullahi, yace sun zargi shugaban da yin watsi da Sakatariya tsawon watanni biyu kuma bai halarci taron zaben fidda ɗan takarar gwamna ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abdullahi ya bayyana cewa Bilal ya gaza kare kansa kan tuhume-tuhumen da ake masa, kana ya tsere daga hakkin dake kansa zuwa Abuja a dai-dai lokacin da jam'iyya ke bukatar sulhunta mambobinta da suka fusata.
Kakakin APC yace:
"Shugaban jam'iyya ya lulluɓe harkokin kuɗi a sirrance kuma yana tafiyar da harkokin jam'iyya kamar mallakinsa ba tare da duba wa da ma'auni ba kuma ba zancen bin diddigi tun da ya ɗare mulki."
"Bayan haka, da gangan shugaban ya ƙi taya 'yar takarar gwamna da ta lashe zaben fidda gwani, Sanata Aishatu Binani, murna a kan lokaci ba tare da wani uzuri ba duk da wasu shugabanni sun shawarci yayi haka."
Wane laifukan cin amana Bilal ya tafka?
Abdullahi ya ƙara da cewa Bilal ya take dokar sashi na 21.2 a kundin mulkin APC inda ya umarci masu kaɗa kuri'a a mazaɓar Sanatan shiyyar arewa su zaɓi jam'iyyar NNPP, kamar yadda Punch ta rahoto.
A cewarsa, shugaban jam'iyyar ya yi amfani da shafinsa na Facebook wajen rokon mutane su kauracewa yar takarar gwamna a inuwar APC, su zaɓi Sanata Ishiaku Cliff Abbo na NNPP.
Haka zalika ya saɓa wa sashi na 23 da aka yi wa garambawul wanda ya kunshi samar da sa hannun shugaban jam'iyya, Sakatare, Ma'ajiya da Sakataren kuɗi a asusun ajiyar jam'iyya.
Da aka tuntube shi ta wayar salula, Bilai bai ɗaga kiran da wakilin jaridar ya masa ba domin jin ta bakinsa game da matakin da kwamitin ya ɗauka a kansa.
A wani labarin kuma Bola Tinubu Ya Tsoma Baki Kan Rikicin Atiku da Wike, Ya Raɗa Wa PDP Sabon Suna
Tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu, yace yana mamakin yadda a kai har yanzun PDP ke raye bayan ta kashe ƙasa.
Ɗan takarar shugaban kasa ya bayyana cewa APC ta shirya tsaf domin magance duk wasu kalubale da suka kewaye Najeriya.
Asali: Legit.ng