2023: Ina Mamaki Meyasa Har Yanzu Basu Tarwatse Ba, Tinubu Yi Yi Wa PDP Shagube

2023: Ina Mamaki Meyasa Har Yanzu Basu Tarwatse Ba, Tinubu Yi Yi Wa PDP Shagube

  • Tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu, yace yana mamakin yadda a kai har yanzun PDP ke raye bayan ta kashe ƙasa
  • Ɗan takarar shugaban kasa ya bayyana cewa APC ta shirya tsaf domin magance duk wasu kalubale da suka kewaye Najeriya
  • Jam'iyyar PDP na fama da rikicin cikin gida musamman tsakanin Atiku Abubakar da gwamna Wike

Abuja - Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar APC, yace yana mamakin yadda har yanzun PDP bata tarwatse ba.

Tsohon gwamnan jihar Legas ya yi wannan furucin ne yayin kaddamar kamfen ɗin Tinubu/Shettima Kofa zuwa Kofa a Abuja, kamar yadda Thecable ta ruwaito.

Bola Ahmed Tinubu.
2023: Ina Mamaki Meyasa Har Yanzu Basu Tarwatse Ba, Tinubu Yi Yi Wa PDP Shagube Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Tinubu bayan bayyana PDP da jam'iyya mara madogara, ya roki mambobin jam'iyyar APC da su ɗauke idonsa game da tsagin adawa.

Kara karanta wannan

2023: Wani Babban Jigon APC da Dubbannin Magoya Baya Sun Sauya Sheka Zuwa PDP

A kalamansa yace:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ba mu ya kamata mu riƙa jifan tsagin adawa da zage-zage da cin mutunci ba, bamu bukatar haka, muna da wayo da basira, muna da kwarin guiwa kuma ba jirgi ɗaya ya kwaso mu da su ba."
"Shekara 16 suna mulki amma sun mance da Titin jirgin ƙasa wanda zai saukaka wa mutane tafiye-tafiye da safarar kayayyaki zuwa lungu da sako na ƙasa. Ina mamaki har yanzu jam'iyyar tana raye."
"Sune mutanen dake yaƙi kan shugabancin jam'iyya, suna laluben hanyar da zata ɓulle musu, ba ɗaya muke da su ba, mun zarce su wayo kuma mun san hanya, mu bar su da lalube a baya. Kar mu damu da PDP, Jam'iyyar cigaban talauci."

Wane shiri APC take yi?

Da yake ƙarin haske kan shirye-shiryen jam'iyyarsa, Tinubu yace APC na da hanyar warware matsalolin Najeriya, inda ya ƙara da cewa jam'iyyar ta shirya magance ƙalubalen ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Rikici: Dole Shugaban Jam'iyya Na Kasa Ya Yi Murabus, Jigon PDP Ya Koma Bayan Wike

"Muna da yaƙini da kwarin guiwar gane matsala da nemo hanyar warware ta domin goben 'ya'yanmu, zamu iya tabbatar muku da yadda gobe zata yi kyau, ayyuka ga jikokinmu da cigaba."

A wani labarin kuma Gwamnan Oyo na PDP ya musanta rahoton cewa ya halarci gangamin taron Peter Obi

Gwamnan jihar Oyo ya musanta jita-jitar da ake yaɗa wa cewa ya halarci gangamin taron magoya bayan Obi a Ibadan.

Sakataren watsa labarai na gwamna Makinde ya ce labarin karya ce da aka shirya da nufin gurbata tunanin mutane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262