Gwamna da Wasu Jiga-Jigai Biyu Sun Kaurace Wa Taron Atiku da 'Yan takarar PDP
- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya gana da 'yan takarar gwamnonin jihohi a inuwar PDP a Abuja
- Sai dai taron ya kara haska ɓarakar PDP domin ba'a hangi yan takara daga jihohin Ribas da Abiya ba da kuma gwamnan Oyo
- Taron ya zo ne a lokacin da gwamna Wike, wanda ke takun saka da jagorrin PDP, ya sake jan tawagarsa zuwa Landan
Abuja - Ɗan takarar gwamnan jihar Ribas a inuwar PDP, Siminialayi Fubara, da takwaransa na jihar Abiya, Uchenna Ikonne, an nemi su an rasa yayin da Atiku Abubakar, ya gana da 'yan takarar gwamna a 2023 ranar Asabar.
Rahoto ya nuna cewa baki ɗaya 'yan takarar biyu, Fubara da Ikonne, sun samu cikakken goyon baya daga gwamna Nyesom Wike da gwamna Okezie Ikpeazu, har suka lashe tikitin takara a jihohinsu.
An gudanar da taron ɗan takarar shugaban kasa da masu neman kujerun gwamnoni a johohi karkashin inuwar PDP a dai-dai lokacin da Wike ya jagoranci wasu gwamnoni zuwa Landan.
Gwamna Wike na takun saka da shugabannin jam'iyyar PDP tun bayan rashin nasararsa a zaɓen fidda gwamnin jam'iyya, wanda ya gudana a watan Mayu.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Rikicin babbar jam'iyyar adawa ta ƙasa ya ƙara tsananta ne bayan Atiku ya zaɓi gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta a matsayin abokin takararsa, inda ya yi fatali da shawarin kwamiti, wanda ya nemi a ɗora Wike a matsayin.
Haka zalika, Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo bai samu halartar taron ba, wanda ya gudana a babban birnin tarayya Abuja ranar Asabar.
Da yake tabbatar ganawar a shafinsa na Facebook, tsohon mataimakin shugaban ƙasan yace taron ya yi nazari kan yanayin ƙasa da kuma yadda za'a jawo hankalin masoya da sauran 'yan Najeriya su mara wa PDP baya.
Atiku yace:
"A yau, na gana da masu neman kujerar gwamna a inuwar PDP a gidana na Abuja. Dama ce ta haska yanayin kasa da yadda a dunkule, zamu tattara 'yan kasa domin cimma burin mu na kawar da jam'iyya mai mulki da fara gina Najeriya."
Su wa suka halarci taron?
Wasu daga cikin waɗanda suka samu halartar taron sun haɗa da, masu neman kujerar gwamna a jihohin Kaduna, Filato, Katsina, Legas, Delta, Yobe, Jigawa, Nasarawa, Kwara, Benuwai, Borno, Ebonyi, Neja, Kano da Sokoto.
A wani labarin kuma Jerin Sunayen Jiga-Jigan PDP Na Kasa Dake Rura Wutar Rikicin Atiku da Wike
Ana zargin tsoffin gwamnoni biyu daga jihohin Ondo da Kuros Riba da jagorantar rura wutar rikicin Atiku Abubakar da gwamna Wike.
Bayan su kuma ana zargin wasu tsofaffin Ministoci, wani Sanata da masu ruwa da tsaki a PDP da ƙara wutar rikicin Fetur.
Asali: Legit.ng