Zaben 2023: Shettima da Gwamna Yahaya Bello Sun Shiga Ganawar Sirri a Abuja
- Gwamnan Kogi, Yahaya Bello, ya gana da tsohon gwamnan Borno, Sanata Kashim Shettima a gidansa dake Abuja
- Sakataren watsa labarai na gwamnan, Onogwu Muhammed, ya ce manyan jiga-jigan APC sun tattauna kan abubuwa masu muhimmanci
- Shettima, shi ne abokin takarar Asiwaju Bola Tinubu, mai neman kujerar shugaban kasa a inuwar APC
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, wanda ya nemi takarar shugaban ƙasa a inuwar APC, da yammacin Litinin ya karɓi bakuncin ɗan takarar mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima a gidansa na Abuja.
Shettima, tsohon gwamnan jihar Borno, shi ne abokin takarar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, na jam'iyyar APC a babban zaɓen 2023 dake tafe.
Wannan na ƙunshe ne a wata gajeriyar sanarwa da Sakataren watsa labarai na gwamnan Kogi, Onogwu Muhammed, ya fitar a shafinsa na Facebook.
Mista Muhammed ya bayyana cewa mai gidansa da kuma baƙonsa (Sanata Shettima) sun, "Gana da juna a taƙaice."
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A cewar sakataren watsa labaran gwamnan, tsaron jiga-jigan biyu, "Ya maida hankali ne kan shirye-shirye da dabarun lashe zaɓen shugaban ƙasa dake tunkaro wa ga jam'iyya mai mulki."
Wani sashin sanarwan ya ce:
"Mai girma gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya karɓi bakuncin tsohon gwamnan Borno, Sanata Kashim Shettima a gidansa dake Abuja da yammacin Litinin."
"Gwamnan da baƙonsa sun sa labule a takaice wanda ya fi maida hankali kan shirye-shirye daban-daban da dabarun yadda jam'iyya mai mulki zata lashe zaɓen shugaban ƙasa a 2023."
A wani labarin kuma Wani Babban Malami Ya Bayyana Sunan Wanda Zai Gaji Buhari a 2023, ya ce sako ne daga Allah
Wani Malami ya bayyana maganar Manzanci cewa ɗan takarar APC, Bola Tinubu , ne zai gaji shugaba Buhari a zaɓen 2023.
A shekarar 2019, Malamin Cocin ya yi hasashen shugaba Buhari zai lashe zaɓe karo na biyu, haka Sanata Omo-Agege.
Asali: Legit.ng