Dan Majalisar Tarayya Daga Ribas Ya Fadi Wanda Zasu Zaba a 2023

Dan Majalisar Tarayya Daga Ribas Ya Fadi Wanda Zasu Zaba a 2023

  • Ɗan majalisar wakilan tarayya na PDP daga jihar Ribas ya mara wa takarar Atiku Abubakar baya a zaben 2023
  • Farah Dagogo ya bayyana shirinsa na haɗa kan mutum miliyan 10m a baki ɗaya Neja Delta don tabbatar da goyon bayan yankin ga Atiku
  • A kwanakin baya jami'an tsaro sun damƙe ɗan majalisar bayan gwamna Nyesom Wike ya zarge shi da rura wutar matsalar yan asiri

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Rivers - Mamban majalisar wakilan tarayya, Farah Dagogo, ya ayyana cikakken goyon bayansa ga ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar PDP, Atiku Abubakar, da abokin takararsa, gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta.

Dagogo, mai wakiltar mazaɓar tarayya Degema/Bonny a jihar Ribas, ya ce nan ba da jimawa ba zai shirya tattakin mutane miliyan 10m a jihohin yankin Neja Delta domin Atiku/Okowa.

Rikicin PDO
Dan Majalisar Tarayya Daga Ribas Ya Fadi Wanda Zasu Zaba a 2023 Hoto: Atiku Abubakar, Wike
Asali: Facebook

Channelst TV ta rahoto a wata sanarwa da hadimin ɗan majalisar, Ibrahim Lawal ya fitar, ya ce zai shirya Macin ne domin nuna wa duniya cewa har yanzu yankin na PDP ne.

Kara karanta wannan

Fitaccen Jarumin Fina-Finai a Najeriya Ya Fice APC, Ya Koma Bayan Wanda Yake So Ya Gaji Buhari a 2023

Dalilin da yasa Neja Delta zata zaɓi PDP, Atiku - Dagogo

Farah Dagogo ya yi fatali da raɗe-raɗin cewa mutanen yankin Neja Delta zasu juya wa PDP baya sakamakon kayen da Gwamna Wike ya sha hannun Atiku a zaɓen fidda gwani da wasu dalilai.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ɗan majalisar ya ce, "Neja Delta ta kasance tare da jam'iyyar PDP tun shekarar 1999 zuwa yau kuma 2023 ba zata zama bare ba."

A cewarsa, mutanen yankin Neja Delta ba zasu mance da yadda jam'iyyar PDP ta yi sanadin samar da shugaban ƙasa daga yankin su watau Goodluck Jonathan.

"Kar ku yarda a yaudare ku, tsarin zaɓen Najeriya yanzun ya canza, karfin iko na hannun masu katin zaɓe. Ba wanda zai yanke wa mutane wanda zasu zaɓa ko waye shi sabida mutane ke da wuka da nama kan katin zaɓen su."

Kara karanta wannan

Sabuwar Matsala a PDP, Ɗan Takarar Gwamna Ya Fice, Ya Koma Bayan Wanda Yake So Ya Gaji Buhari a 2023

Ɗan majalisar ya kara da cewa Atiku zai lashe zaɓe domin haka ne ribar waɗan da ba su son a barsu a baya ko a watsar da su a kwandon sharar jam'iyya.

Rikicin Dagogo da Wike

A watan Afrilu, Gwamna Wike ya ayyana nema da kame Dagogo duk inda aka ganshi bisa zargin ɗaukar nauyin ƴan asiri su tarwatsa taron tantance yan takarar PDP a Sakatariya da ke Patakwal.

Ɗan majalisar, wanda ke neman takarar gwamna karkashin inuwar PDP a wancan lokacin, ya shiga hannun jami'an tsaro bayan umarnin Wike.

Sai dai Babbar Kotu a Patakwal ta bayar da Belinsa kan miliyan N20m bayan shafe kusan wata ɗaya ana kai ruwa rana a shari'ar.

A wani labarin kuma Gwamnatin Buhari Ta Baiwa Kamfanoni Biyu Kwangilar Makudan Kuɗi Don Tsare Titin Jirgin Ƙasan Abuja

Gwamnatin tarayya ta amince da ware miliyan N718.16 domin aikin tsaron Titin Jirgin kasa dake birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Bayan Tinubu Ya Gana Da Gwamnonin PDP, Na Hannun Daman Gwamna Ya Sauya Sheka Zuwa APC

Ministan Abuja, Muhammad Bello, ya ce an baiwa Kamfanoni biyu kwangilar ba da tsaro a layin dogon mai tsawon kilomita 45.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262