Ministan Buhari Yace Zai Iya Tuka Mota daga Abuja Zuwa Kaduna Ba Jami'an Tsaro

Ministan Buhari Yace Zai Iya Tuka Mota daga Abuja Zuwa Kaduna Ba Jami'an Tsaro

  • Karamin ministan kwadago da ayyukan yi, Festus Keyamo, ya bugi kirji inda yace zai iya tuka mota tun daga Abuja har zuwa Kaduna
  • Ministan wanda shi ne mai magana da yawun tawagar kamfen din APC ta kasa, yace babu ko jami'in tsaro daya zai tuko daga Abuja har Kaduna
  • Ya jaddada cewa, shugaba Buhari yayi kokari a fannin tsaro don ya nakasa Boko Haram ta yadda ana iya bin titunan Borno da aka rufe a baya

FCT, Abuja - Festus Keyamo, karamin ministan kwadago da aikin yi, yace zai iya tuka mota tun daga Abuja har Kaduna ba tare da masu tsaron lafiyarsa ba.

Keyamo ya sanar da hakan ne a ranar Talata a wata tattaunawa da yayi da gidan talabijin na Channels.

Tafiyar mai nisan kilomita 155 kan babbar hanyar tana daya daga cikin titunan dake da hatsari kuma ake fuskantar manyan farmakin 'yan ta'addan dake tare mutane tare da garkuwa da su.

Kara karanta wannan

Shiga siyasa: Matasa a Abuja sun kama wani Bishap, sun lakada masa dukan tsiya

A ranar 28 ga watan Maris, jirgin kasa da ya debo fasinjoji daga Abuja zai kai su Kaduna ya fuskanci hari a jihar Kaduna. 'Yan ta'addan sun halaka mutane yayin da suka yi garkuwa da wasu a farmakin, TheCable ta rahoto.

Amma Keyamo, wanda shi ne mai magana da yawun tawagar kamfen din jam'iyyar APC, yayin da aka tambaye shi kan tsaron Najeriya, yace hankali kwance zai tuka mota a titin babu jami'an tsaro.

"Wasu suna yin hakan, nima zan iya. Zan iya hakan," Keyamo ya maimaita.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Na ga kanun labarai a makon da ya gabata ana cewa nace Buhari ya durkusar da rashin tsaro. Ban ce haka ba. Har yanzu yayin kanun labaran karya ake yi. Nace abinda muka tarar a Arewa maso gabas ne na Boko Haram. Na banbance amma sai aka sauya zancen. Nace Boko Haram a Arewa maso gabas bata kare ba, ta ragu da sosai.

Kara karanta wannan

Yadda Shehin Malami ya Taimaki Wanda Bai Sani ba, Ya Kare da Halaka shi

"Dukkan titunan da suka shiga Chibok zuwa Damboa a jihar Borno ana iya wucesu yanzu."
"Batun rikicin manoma da makiyaya yayi kamari tsakanin 2017 zuwa 2020. Kiyasin ta'addanci na duniya ne ya tabbatar da hakan ba ni ba. Ya kuma kara tabbatar da cewa ya ragu sosai a 2021, ya kara raguwa a 2022.
"A bangaren 'yan bindiga da garkuwa da mutane, hakan suke a yankin arewa maso yamma da wasu sassan arewa ta tsakiya. Wannan na yadda."

Yadda 'Yan Bindiga Sun Kallafawa Manoman Kaduna Harajin Miliyoyin Naira

A wani labari na daban, manoman karamar hukumar Birnin Gwari dake jihar Kaduna sun amince zasu biya makuden kudaden da 'yan bindiga suka kallafa musu in har suna son amfani da gonakinsu.

Kamar yadda Ishaq Usman Kasai, shugaban kungiyar masarautar Birnin Gwari, yace 'yan bindigan sun kallafa musu harajin miliyoyin naira kan manoman, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kamar almara: Sauyawar wani matashi daga sana'ar acaba zuwa tauraro ya ba da mamaki

A wata takarda, yace manoman sun sun yanke hukuncin yin ciniki da 'yan bindigan saboda basu da wata mafita.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng