2023: Jagoran APC, Bola Tinubu, Zai Gana da Tsohon Shugaban Kasa Obasanjo Yau
- Ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Tinubu, ya shirya gana wa da Obaasanjo yau a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun
- Bayanai sun nuna cewa jim kaɗan bayan tattaunawarsa da tsohon shugaban, Tinubu zai yi jawabi ga mutane a filin MKO Abiola
- Wannan shi ne karo na uku da tsohon gwamnan Legas ke kai ziyara Ogun a shirinsa na gaje Buhari a 2023
Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa karkaashin inuwar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, zai gana da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, yau Laraba a Abeokuta, jihar Ondo.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa taron wani ɓangare ne na ziyarar neman shawari da ɗan takarar ke yi domin cimma burinsa na zaman shugaban kasa a 2023.
Sakataren watsa labarai na gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun, Kunle Somorin, shi ne ya bayyana haka yau Laraba da safe.
A rahoton Leadership, Somorin ya ce:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Mun fahimci cewa ɗan takarar shugaban ƙasa karkashin APC, Asiwaju Bola Tinubu, zai kawo ziyara Abeokuta, jihar Ogun, yau Laraba, 17 ga watan Agusta, 2022."
"Ya tsara zai sa labule da tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, da misalin ƙarfe 10:00 na safe sannan ya yi jawabi ga mutane a filin ƙasa-da-ƙasa MKO Abiola jim kaɗan bayan kammala wa."
APC ta tabbatar da ziyarar
A wata sanarwar ta daban da shugaban APC reshen Ogun, Yemi Sanusi, ya fitar ya ce, "Baki ɗaya mambobin kwamitin gudanarwa da shugaban jam'iyya na jiha zasu halarta."
"Asiwaju zai shigo Ogun: Muna sanar da cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Tinubu, zai kawo ziyara Abeokuta, jihar Ogun, yau Laraba. Dukkan shugabanni da shugaban jam'iyya su halarta da wuri ƙarfe 10:00 na safe."
Legit.ng Hausa ta gano cewa wannan shi ne karo na uku da tsohon gwamnan zai kai zuyara Ogun kan burinsa na zama shugaban ƙasa.
A wani labarin kuma Yan majalisu biyu da dubbannin yan siyasa sun sauya sheka zuwa PDP a gangamin Atiku
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya karbi dubbannin mambobin jam'iyyu da suka koma PDP a Adamawa.
Atiku Ya kai ziyara mahaifarsa a karon farko tun bayan lashe tikitin takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP.
Asali: Legit.ng