Ku Nemi Taimakon Ubangiji Kan Al'amuran Siyasarmu, IBB Ga 'Yan Najeriya

Ku Nemi Taimakon Ubangiji Kan Al'amuran Siyasarmu, IBB Ga 'Yan Najeriya

  • Tsohon shugaban kaasar Najeriya, Ibrahim Badamasi Babangida, ya yi kira ga 'yan Najeriya da su nemi daukin Ubangiji a lamurran siyasa
  • A yayin zantawa da manema labarai a gidansa dake Minna a ranar Laraba, IBB yayi kira kan hadin kasar nan tare da fatan komai zai daidaita nan babu dadewa
  • Ya yi kira ga manema labarai da su yi watsi da masu yada kiyayya da rabewar kai ta hanyar dakile hanyoyin da suke yada su

Minna, Niger - Ibrahim Babangida, tsohon shugaban kasar Najeriya na mulkin soja, yace 'yan Najeriya su nemi taimakon Ubangiji kan alkiblar da zasu dosa a al'amuran siyasar kasar nan.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa, Babangida ya sanar da hakan ne a ranar Talata yayin zantawa da manema labarai a Minna, babban birnin jihar Niger domin tunawa da zagayowar ranar haihuwarsa.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari: APC ta gyara kasar nan, kamar ba a taba ta'addanci ba

IBB Nigerians
Ku Nemi Taimakon Ubangiji Kan Al'amuran Siyasarmu, IBB Ga 'Yan Najeriya. Hoto daga thecableng
Asali: UGC

Tsohon shugaban kasan ya cika shekaru 81 a ranar 17 ga watan Augustan 2022.

A jawabinsa, yayi kira ga 'yan Najeriya da su cigaba da yin imani wurin hadin kan kasar nan tare da mayar da hankali da sa ran cewa komai zai daidaita.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Ina kira garemu da mu yi hakuri da juna kuma mu kasance masu addu'a kan taimakon Ubangiji a fannin tattalin arziki da siyasa," yace.
“Akwai bukatar mu cigaba da ganar da mutane kan yadda za a zauna lafiya da rikon amana saboda kwanciyar hankali, cigaba da kuma cigaban zamanmu kasa daya."

Ya kara da shawartar kafafen yada labarai da su taimaka wurin habaka hadin kan kasar nan.

“Ku kara zage damtse wurin kokarin canza Najeriya. Idan kafafen yada labarai da manema labarai suka yi burus da masu yada kiyayya, ba zasu samu kafar mika sakonninsu ba," Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito.

Kara karanta wannan

Kaunar da Nake wa 'Yan Najeriya Bata Misaltuwa, Shugaba Buhari

"Kuna kokari wurin ganin cigaba da hadin kan kasar nan. Za ku iya canza tunanin 'yan Najeriya.
“Ina kira gareku da ku yi watsi da wadanda ke yada kiyayya da rabewar kai. Ku yi watsi da su kuma kada ku damu da su. Za ku iya yin hakan ne ta hanyar gyara rahotanninku kuma ina son irin muhawarar dake faruwa yanzu a kafafen yada labarai.
“Wannan na bai wa jama'a haske kan abinda ya dace su gani. Abinda kafafen yada labarai suke yi yanzu yana da kyau sosai."

Kaunar da Nake wa 'Yan Najeriya Bata Misaltuwa, Shugaba Buhari

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake jaddada burin mulkinsa na Inganta rayuwar 'yan kasa duk da matsin tattalin arzikin da ake fama da shi.

Ya ce burinsa na inganta rayukan 'yan Najeriya bai dishe ba, inda yake kira da 'yan Najeriya da su kara hakuri, jaridar Daily Nigerian ta rahoto.

Kara karanta wannan

Goodluck Jonathan ya Fadakar da Mutane a kan Shugabannin da ba za a Zaba a 2023 ba

Shugaban kasan ya bayar da tabbacin hakan ne lokacin da ya karba bakuncin tsohon shugaban tsohuwar jam'iyyar CPC a gidan gwamnati a Abuja, ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng